Dan majalisa ga FG: Makuden kudi kafintoci da direbobi ke samu, a wajabta musu haraji

Dan majalisa ga FG: Makuden kudi kafintoci da direbobi ke samu, a wajabta musu haraji

  • Dan majalisar wakilai daga jihar Osun ya shawarci gwamnati da ta sanya wa kafintoci da direbobi haraji
  • A cewar Fakeye Olufemi dan jam'iyyar APC, ya ce makuden kudade 'yan Najeriya suke samu, don haka su bada haraji
  • Dan majalisar ya ce a lokacin da ya ke yaro, hatta manoma da masu sana'ar dogaro da kai suna biyan haraji

FCT, Abuja - Fakeye Olufemi, dan majalisar wakilan Najeriya, ya ce masu kanana da matsakaitan kasuwanci da suka hada da kafintoci da direbobin tasi ya dace a kallafa musu haraji.

Olufemi dan majalisa ne mai wakiltar Boluwaduro/Ifedayo/Ila a tarayya kuma dan jam'iyyar APC daga jihar Osun. Ya mika wannan bukatar ne a ranar Laraba gaban majalisar, TheCable ta wallafa.

Kara karanta wannan

Jerin sunayen jihohin Najeriya 12 da UK ta shawarci 'yan kasar ta da su kiyaya

Dan majalisa ga FG: Makuden kudi kafintoci da direbobi ke samu, a wajabta musu haraji
Dan majalisa ga FG: Makuden kudi kafintoci da direbobi ke samu, a wajabta musu haraji. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

TheCable ta ruwaito cewa, dokar kudi ta 2020 ta tsame dukkan kananan kamfanoni daga biyan harajin kowacce shekara.

A gudumawar Olufemi kan kasafin kudin shekara ta gaba yayin zaman majalisar, ya ce hakan zai bada gudumawa ga gwamnatin tarayya wurin habaka kudaden shiga.

"Ina son sanar da majalisar cewa, idan za a yi rance ne domin ayyukan shekarar, a dinga arowa daga Janairu, Fabrairu da Maris ba wai a dinga shirya yin rance a tsakiya ko karshen shekarar ba.
“Ina sane cewa a yanzu kudin wata shidan farko na shekarar nan aka saki, ga shi yanzu mu na wata ukun karshe. Wannan kuwa zai kasance kamar kalubale ga ayyukanmu".

Dan majalisar ya kara da cewa:

“A lokacin da na ga gwamnati ba ta samun kudaden shiga, sai na fara tambayar kaina tare da tuna lokacin ina yaro. Kowa ya na biyan haraji. Ko kai manomi, kafinta ko dai wacce irin sana'a ka ke, ka na biyan haraji.

Kara karanta wannan

Hon Sha'aban: Da a yau za a yi zaben gwamna a Kano, warwas za a yi wa APC

“A yanzu kusan an yafe wa kowa haraji, sai dai wadanda ke samun kudi daga inda ake karbar harajin
“Ina tunanin gyaran da za a yi na dokokin haraji, ya dace a ce kowanne dan Najeriya sai ya bada gudumawa. A duba kashi tamanin zuwa casa'in na 'yan Najeriya, da yawansu aikin dogaro da kai suke, ba su biyan haraji."
“A matsayin ka na kafinta, direban tasi, mai siyar da kayayyaki a kasuwa, ya dace ka biya haraji. Wadannan mutanen suna samun makuden kudi amma ba su biyan komai."

Majalisa ta amince da kato bayan kato kadai a zabukan fidda gwanin jam'iyyu

A wani labari na daban, majalisar dattawan Najeriya ta aminta da gyaran dokar zabe wacce ta amince wa jam'iyyun siyasa da su koma zabukan fitar da gwanaye ta hanyar zabukan kato bayan kato.

The Nation ta ruwaito cewa, majalisar tun farko ta amince da dokar zaben da ta amince wa jam'iyyun siyasa su yi zaben kato bayan kato ko kuma zaben fitar da gwani ta hanyan amfani da wakilan jam'iyya.

Kara karanta wannan

EFCC ta gurfanar da Yarima a gaban kotu kan badakalar N35.5m

Wannan hukuncin ya biyo bayan majalisar dattawan da ta karba wata bukata wacce Sanata Yahaya Abdullahi daga Kebbi ta arewa ya mika gaban majalisar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel