Mun rabawa matasan Najeriya 7,057 tallafin N3bn ta shirin NYIF, CBN

Mun rabawa matasan Najeriya 7,057 tallafin N3bn ta shirin NYIF, CBN

  • Hukumar kididdigan Najeriya ta bayyana cewa adadin mazauna Najeriya matasa ne masu shekaru 15 zuwa 34 kimanin milyan 100 ne
  • Daga cikin wannan adadi, hukumar Lissafi da bincike NBS ta ce kawo karshen 2020, kashi 38.5% na matasa basu da aikin yi
  • Saboda haka gwamnatin tarayya ta samar da tallafin matasa (NYIF) karkashin Ma'aikatar matasa da wasanni

Abuja - Babban bankin Najeriya (CBN), yace a shirin da yake yi tare da ma'aikatar matasa da wasanni, kawo yanzu an rabawa matasan Najeriya 7,057 kudi N3bn.

An yiwa shirin take 'Asusun lamunin matasan Najeriya' (NYIF).

Wannan na kunshe cikin rahoton da CBN ya wallafa a shafinsa ranar Litinin, 11 ga Okotba, 2021.

A cewar rahoton, wadanda suka amfana da wannan kudi sun hada da daidaikun mutane 4,411, da kuma masu kananan sana'o'i 2,646.

Kara karanta wannan

Daukar aikin dan sanda: Za'a fitar da sunayen wadanda sukayi nasara a mataki na farko

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mun rabawa matasan Najeriya 7,057 tallafin N3bn ta shirin NYIF, CBN
Mun rabawa matasan Najeriya 7,057 tallafin N3bn ta shirin NYIF, CBN Hoto: Aso Rock
Asali: Twitter

Menene tallafin NYIF?

Bankin CBN ya fara shin NYIF ne a yunkurin da takeyi na baiwa matasa yan kasuwa tallafi domin samar da aikin yi wanda zai rage zaman kashe wando tsakanin matasa.

Rahoton ya kara da cewa NYIF na neman matasa masu shekaru tsakanin 18 da 35 don basu jarin kasuwanci.

Yace:

"Muna neman matasa masu ayyukan hannu da kananan kasuwanni wadanda zasu zama masu gidan kansu kuma su samar da ayyuka akalla 500,000 tsakanin 2020 da 2023."

Tattalin arziki: Mataimakin Shugaban kasa, Osinbajo ya yi wa Gwamnan CBN kaca-kaca

Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya soki tsarin da babban bankin Najeriya na CBN ya dauka a kan batun canjin kudin kasashen waje.

Premium Times tace Yemi Osinbajo ya ba babban bankin kasar shawara ya sake tunani kan batun canji.

Kara karanta wannan

A tura matasan NYSC faggen yaki da yan bindiga, wanda ba zai je ba a daina biyansa albashi

Da yake magana a wajen taron bitar da aka shirya wa Ministoci a ranar Litinin, 11 ga watan Oktoba, 2021, Farfesa Osinbajo ya kawo wannan batun.

A cewar Farfesa Yemi Osinbajo, farashin Naira ya yi kasa sosai a kasuwar canji, wanda a cewarsa hakan ba shi ne asalin zahirin abin da yake kasuwan ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel