Duk da komawa APC, da alamu Fani-Kayode zai fuskanci fushin kotu saboda badakala

Duk da komawa APC, da alamu Fani-Kayode zai fuskanci fushin kotu saboda badakala

  • Femi Fani-Kayode na fuskantar shari'a a wata kotu a jihar Legas bisa zargin halatta kudin haram
  • A halin da ake ciki, yana karkashin beli, wanda alkali ya bayyana yiyuwar soke wannan belin
  • Fani-Kayode bai halarci kotu ba, lamarin da ya fusata alkali ya bayyana sabon mataki kan batun

Legas - Babbar Kotun Tarayya da ke zama a Legas ta umarci tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Femi Fani-Kayode, da ya biya tarar N200,000 saboda rashin halartarsa a sake gurfanar da shi da aka yi ko kuma ya fuskanci soke belinsa.

Gidan talabijin na Channels ya rahoto cewa, mai shari’a Daniel Osaigor ya ba da umurnin ne a ranar Laraba, yana mai cewa bayan ya duba fayil din kotun, ya lura da wasiku daban-daban guda biyar da ke neman a dage zaman a kan dalilan rashin lafiya.

Kara karanta wannan

An yanke wa Salisu ɗaurin gidan yari kan satar tukwane da kujeru a coci a Legas

Duk da komawa APC, da alamu Fani-Kayode zai fuskanci fushin kotu saboda badakala
Femi Fani-Kayode | Hoto: guardian.ng
Asali: Twitter

Hukumar EFCC ce ta gurfanar da Fani-Kayode tare da tsohon karamin ministan kudi, Nenandi Usman, da wani Danjuma Yusuf, tsohon shugaban ALGON, da wani kamfani, Jointrust Dimensions Nigeria Limited a gaban kotun.

EFCC ta mika laifuka 17 na halatta kudin haram da suka kai naira biliyan 4.6 akan su a gaban mai shari'a Mohammed Aikawa wanda da farko shine alkalin shari'ar kuma daga baya aka canza shi daga yankin Legas.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Duk da haka, sun musanta laifin da ake tuhumar su da shi kuma an bayar da belin su.

Daga baya aka shigar da karar a gaban sabon alkali, mai Shari'a Osaigor, kuma an shirya sake gurfanar da wadanda ake karan a ranar Laraba (13 ga Oktoba).

Idan baku manta ba, Femi Fani-Kayode ya koma jam'iyyar APC, lamarin da ya jawo cece-kuce, har wasu ke ganin daga nan ya tsallake duk wata tuhuma.

Kara karanta wannan

EFCC ta gurfanar da Yarima a gaban kotu kan badakalar N35.5m

Daga shigarsa APC, an ga fostar Femi Fani-Kayode yana neman Mataimakin Shugaban kasa

Hotunan neman takarar gwamna Yahaya Bello da tsohon Ministan harkokin jiragen sama, Femi Fani-Kayode suna yawo a kafofin sadarwa na zamani.

A ranar Lahadi, jaridar Independent ta kawo rahoto cewa wadannan fastoci suna dauke da taken “Yahaya and Femi 2023” tare da tambarin jam’iyyar APC.

Fastocin sun nuna Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello yana neman kujerar shugaban kasa, yayin da Femi Fani-Kayode ya tsaya a matsayin mataimakinsa.

Nigeria youths Awareness Group mai goyon bayan takarar Yahaya Bello ta fito tayi magana, inda ta nesanta kanta daga fastocin da suka fara yawo a kasar.

Sauya-shekar FFK ta yi farin jini?

Makwannin da suka gabata ne aka tabbatar da cewa tsohon Ministan ya koma APC. Sai dai wasu jiga-jigan APC da PDP duk sun la’anci sauya-shekar da Fani-Kayode ya yi.

Kara karanta wannan

Wani mutum ya datse 'yar yatsar jami'in ɗan sanda da cizo a Legas

Irinsu Reno Omokri sun ce PDP ta samu wanda ya fi Femi Fani-Kayode washegarin komawarsa Jam’iyyar APC, ganin cewa Sanata Shehu Sani ya shiga PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel