Bill Gates ya sake gwangwaje tsohuwar matarsa da kadarori na makuden kudi bayan sakinta

Bill Gates ya sake gwangwaje tsohuwar matarsa da kadarori na makuden kudi bayan sakinta

  • Duk da rabuwar aurensu, alamu suna nuna cewa Bill Gates zai rike alkawarin da ya dauka a ranar Laraba, 4 ga watan Augusta
  • Dama ya dauki alkwarin cigaba da yin aiki da tsohuwar matarsa Melinda French Gates akan cigaba da bunkasa gidauniyarsu
  • A ranar Alhamis, 5 ga watan Augusta Bill Gates ya turawa Melinda kadarar da ta wuce dala biliyan 2 kamar yadda Bloomberg ta ruwaito

Washington, Amurka - Duk da rabuwar auren Bill Gates da matarsa Melinda French Gates, alamu suna nuna cewa ya rike alkawarin da ya dauka a ranar Laraba, 4 ga watan Augusta lokacin da CNN take hira dashi har yace zasu cigaba da yiwa gidauniyarsu aiki duk da sun rabu.

Bill Gates ya turawa Melinda kadara wacce ta zarce ta dala biliyan 2 a ranar Alhamis, 5 ga watan Augusta kamar yadda Bloomberg ta ruwaito.

Bill Gates ya sake gwangwaje tsohuwar matarsa da kadarori na makuden kudi bayan sakinta
Bill Gates ya sake gwangwaje tsohuwar matarsa da kadarori na makuden kudi bayan sakinta. Hoto daga lindaikejisblog.com
Asali: UGC

Kenan Bill Gates ya tura mata dala biliyan 6 tun bayan rabuwar aurensu, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

Kara karanta wannan

Kyari-Hushpuppi: An zargi Dino Melaye da karbar na shi rabon $31m, ya karyata

Dalla-dallar bayanin kadarorin da kudaden suka shafa

Hannun jarin Cascade, hannun jarin ababen hawa, ya tura kudin hannayen jari miliyan 3.3, gaba daya idan aka hada dala miliyan 387 da sauran hannayen jari, kamar yadda Bloomberg suka ruwaito.

Sannan Bill Gates ya tura hannayen jari miliyan 2.8 masu kimar dala biliyan daga zuwa ga manufacturer Deere & Co. zuwa ga Melinda French Gates ta Cascade Investment kamar yadda Bloomberg ta ruwaito.

A rana daya Cascade Investment ta tura hannayen jari miliyan 9.5 mai kimar fiye da dala biliyan daya da Canadian National Railway zuwa ga Melinda French Gates, shafin Linda Ikeji ya tabbatar.

A makon da ya gabata Bill Gates da Melinda French Gates suka rabu.

A watan Mayu, bayan kwana 4 da suka bayyana kudirinsu na rabuwa, Bill Gates ya tura kadarori masu kimar dala biliyan 3 daga Cascade Investment zuwa ga French Gates, duk da hannayen jari miliyan 2.9 na AutoNation, sai hannayen jarin Canadian National Railway guda miliyan 14.1 da kuma hannayen jari 293.5 na Media Company Grupo Televisa.

Kara karanta wannan

Ranar kin dillaci: EFCC ta karbe manyan gidaje, motoci da miliyoyi a hannun wasu ‘Yan damfara 2

Bayan makonni biyu, Gates suka tattara hannayen jari na Deere & Co. masu kimar dala miliyan 850 zuwa ga Melinda French Gates a cewar SEC filling- wannan kaso 7 bisa dari kenan na dukiyar Gates a cikin kamfanin.

Gaba daya Bill da Melinda Gates suna da dukiya mai kimar dala biliyan 152 kamar yadda Bloomberg ta ruwaito.

Shekara 1 da aure: Hoton dankareriyar motar da mijin Adama Indimi ya gwangwajeta da ita

Hamshakin mai kudin nan, mijin Adama Indimi kuma yariman Kogi, Malik Ado-Ibrahim ya gwangwaje matarsa da kyautar mota a ranar da suka cika shekara daya da aure.

Masoyan wadanda suke shagalin cika shekara daya tare a ranar Lahadi, 8 ga watan Augusta sun tafi wani wuri wanda basu bayyana ba don su cigaba da shagalin.

A shekarar da ta gabata ne aka yi gagarumin shagalin bikin diyar biloniyan Maiduguri da yarima Malik-Ado Ibrahim.

Asali: Legit.ng

Online view pixel