Yanzu-Yanzu: Attajirin Duniya Bill Gates Ya Saki Mai Ɗakinsa Melinda

Yanzu-Yanzu: Attajirin Duniya Bill Gates Ya Saki Mai Ɗakinsa Melinda

- Attajirin duniya, Mr Bill Gates da matarsa Belinda Gates sun sanar da mutuwar aurensu

- Bayan shekaru 27 suna zaman aure, Bill da Melinda Gates sun ce sun kai wani mataki da ba za su iya cigaba da auren ba

- Bill da Melinda Gates sun ce za su cigaba da aiki tare a gidauniyarsu ta Bill and Melinda Gates Foundation

Bill Gates, attajirin duniya kuma wanda ya kafa kamfanin kwamfuta na Microsoft ya sanar da shirinsa na rabuwa da mai dakinsa Belinda.

Bill da Melinda sun sanar da labarin ne a shafukansu na Twitter a ranar Litinin inda suka ce sun dauki wannan matakin ne bayan nazari sosai.

Yanzu-Yanzu: Attajirin Duniya Bill Gates Ya Saki Mai Ɗakinsa Melinda
Yanzu-Yanzu: Attajirin Duniya Bill Gates Ya Saki Mai Ɗakinsa Melinda. Hoto: @BillGates/@MelindaGates
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Yadda Muka Hana a Yi Wa Matasan Arewa 45 Kisar Gilla a Ondo, Amotekun

Ma'auratan sun dade suna jagorantar ayyuka da dama na taimakon jama'a a sassan kasashen duniya daban-daban.

A cikin sanarwar da suka fitar na rabuwarsu, sun ce za su cigaba da aiki tare a gidauniyarsu na Bill and Melinda Gates Foundation.

Yayin aurensu na tsawon shekaru 27, sun haifi yara uku.

"Bayan nazari mai zurfi da aiki kan zaman aurenmu, mun cimma matsayar kawo karshen auren," a cewar sanarwar.

A cikin shekaru 27 da suka gabata, mun haifi yara uku sannan mun kafa gidauniya da ke ayyuka a sassan duniya domin inganta rayuwan mutane.

KU KARANTA: Da Ɗuminsa: An Damƙe Wanda Ake Zargi da Ɗaukan Nauyin Kai Hare-Hare a Imo

"Za mu cigaba da aiki tare domin cimma wannan manufar a gidauniyarmu amma ba za mu iya cigaba da kasancewa ma'aurata a yayin da za mu shiga matakai na gaba a rayuwarmu.

"Muna rokon a bamu sarari tare da mutunta sirrinmu a yayin da iyalin mu ke shiga wannan sabon rayuwar."

A wani labarin daban kunji wasu matasa a Daura, a ranar Alhamis 29 ga watan Afrilu sun kaddamar da kungiyar ta goyon bayan Dr Abubakar Bukola Saraki ya fito takarar shugabancin kasa a zaben 2023, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban kungiyar, Abubakar Nuhu Adam, ya ce sun yanke shawarar kafa kungiyar na goyon bayan tsohon shugaban majalisar ya yi takarar shugaban kasa ne saboda abin da ya yi da kuma abubuwan da ya ke yi wa matasa a kasar.

Hon. Adam ya bada misali dokar 'Not Too Young To Run' da aka aiwatar lokacin Saraki na shugabancin majalisa da kuma goyon bayan da ya bawa matasa su yi takarar kwamitin zartawar na jam'iyyar PDP da wasu sauransu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel