Matashi Ya Tafi Tono Kabarin Abokinshi Saboda Ya Mutu Masa da Kudi N1.5bn

Matashi Ya Tafi Tono Kabarin Abokinshi Saboda Ya Mutu Masa da Kudi N1.5bn

  • Matashi ya ba da mamaki bayan ganinshi a makabarta ya je tono kabarin abokinshi don bashin kudade
  • Matashin ya ce abokin nasa ya mutu masa da wasu kudade har Dala miliyan 2 bayan ya gama shan wahala a baya
  • A faifan bidiyon, matashin ya bayyana cewa sun yi wani harka ne da abokin nasa ta makudan kudade amma sai ya mutu bai biya shi ba

Wani matashi dan Najeriya ya gagara hakuri bayan abokinsa ya mutu ba tare da biyashi bashin da ya ke bin shi ba.

A cikin wani faifan bidiyo, an gano matashin a bakin kabari ya na ta kuka inda ya ce ya mutu masa da Naira biliyan daya da rabi.

Matashi ya tono abokinshi a kabari kan kudaden da ya mutu masa da su
Matashin kenan yayin da ya ke kokarin tono abokinshi. Hoto: @mediagist/Instagram.
Asali: Instagram

Meye matashin ke cewa kan abokinshi?

Ya bayyana cewa sun yi wata harka ce ta kasuwa inda su ka samu makudan kudade.

Kara karanta wannan

“Ba a Jin Kanmu”: Kawaye Biyu Na Soyayya Da Saurayi Daya, Sun Yi Sharholiya Da Shi a Bidiyo

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce ya kamata abokin nasa ya ba shi Naira biliyan daya da rabi ne amma ya mutu da kudaden.

Yayin da ya gagara hakuri, matashin ya tafi kabarin abokin nasa da cebur inda ya fara tono shi don karbar kudadenshi ta ko wane hanya.

A cikin faifan bidiyon, an jiyo shi ya na cewa:

"Azaman, ka na da karfin halin da za ka gudu min da Dala miliyan 2, me yasa ba ka mutu ba lokacin da nake shan wahala.

Wannan abin da matashin ya yi a faifan bidiyo ya jawo martanin mutane da dama.

Ku kalli bidiyon a kasa:

Legit ta tattaro muku martanin mutane inda su ka tofa albarkacin bakinsu, wasu na cewa mutuwar karya ya yi kawai.

@beatrice_konadu1:

"Watakila Azaman mutuwar karya ya yi don cinye kudaden, daman Azaman mugu ne."

Kara karanta wannan

Matashi Ya Budu Asusun Banki Don Yaran da Zai Haifa Su 6, Ya Ajiye N2.4bn, Ya Fadi Abin da Zai Tara a Bidiyo

simeon.delight:

"Azaman ba zai ji kanshin aljanna ba."

@penny_gramss:

"Azaman bai mutu ba, zai je Dubai hutu."

@molarry_:

"Kowa ya yi tafiya kawai."

Budurwa ta haura kofar shiga gida don kai gulma

A wani labarin, wata budurwa 'yar Najeriya ta ba da mamaki bayan an gano ta cikin hatsari a kokarin isar da sakon gulma.

Budurwar ta haura kofar shiga gidan wanda ke dauke da wayoyin lantarki kawai don ta kai gulma ga kawarta da ke cikin gidan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel