“Uwa Ko Budurwa?”: Bidiyon Mahaifiyar Wani Katon Matashi Ya Jawo Cece-Kuce A Intanet

“Uwa Ko Budurwa?”: Bidiyon Mahaifiyar Wani Katon Matashi Ya Jawo Cece-Kuce A Intanet

  • Matashi ya girgiza intanet bayan wallafa faifan bidiyo da mahaifiyarsa wacce ta ke ‘yar karama kamar budurwarsa
  • Matashin @anh_vinn a cikin faifan bidiyon ya kalli mahaifiyar tasa cikin mamaki inda ya ce wai ita ce mahaifiyata?
  • Mutane da dama sun yi martini bayan ganin faifan bidiyon inda mafi yawansu su ka yi tsammanin budurwarsa ce

Wani matashi ya hargitsa kafafen sada zumunta bayan ya wallafa faifan bidiyo tare da da mahaifiyarsa a Tiktok.

Matashin @anh_vinn a faifan bidiyon ya kalli mahaifiyarsa cikin mamaki inda ya ke tunanin ya aka yi wannan ‘yar karamar ta haife shi.

Matashi ya girgiza intanet bayan mamakin yadda 'yar karamar mahaifiyarsa ta haifesa
Bidiyon Mahaifiyar Wani Katon Matashi Ya Jawo Cece-Kuce A Kafar Sadarwa Ta Intanet. Hoto: @anhvinn/TikTok.
Asali: TikTok

Mahaifiyar matashin ta yi mamakin dan nata

A martaninta, mahaifiyar ta kalli dan nata cikin alamun shakku bayan ta fahimci dan ya zura mata idanu, Legit.ng ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Matar Aure Ta Kadu Yayin da Ta Isa Wajen Bikin Mijinta, Aminiyarta Ce Amaryar Da Ya Yi

Mafi yawan mutane sun yi mamakin cewa wannan ita ce mahaifiyarsa, inda su ke tsammanin ai budurwarsa ce ganin yadda suke kai daya.

Vinn ya ce:

“Mamakin yadda aka yi ta kasance mahaifiya ta, ta samar da dalibin Kwaleji guda,”

Ku kalli bidiyon a kasa:

Martanin mutane da dama kan matashin da mahaifiyarsa

Mutane da dama sun bayyana ra’ayinsu inda wasu ke tunanin ai matar da suke tare budurwarsa ce.

@gera:

“Dan uwa na dauka budurwarka ce a.”

@gust_yourg:

“Na dauka matarka ce ai.”

@TheOne:

“Kai gaskiya ta na da kyau sosai.”

@Moona:

“Ni ma ina ta mamaki fa.”

@Robloxstories:

“Ka tabbatar mahaifiyarka ce?”

@Melisa Gutierrez:

“Gaskiya ta hadu kuma ta iya wanka.”

@Hope:

“Ina mamakin yadda za ta zama mahaifiyarka, ga ta ‘yar karama kamar kanwarka.”

Budurwa Ta Nuna Kyautar Da Saurayinta Ya Mata Tsawon Shekaru 11, Bidiyon Ya Yadu

A wani labarin, wata budurwa ta wallafa wani faifan bidiyo inda ta nuna irin kyautar da wani saurayinta mai mako ya yi mata a tsawon shekaru 11 da suka yi suna soyayya.

Kara karanta wannan

Babban Sanata Ya Bayyana Yadda Ya Rasa Mahaifinsa Sakamakon Sakacin Likitan Asibiti Mai Zaman Kansa

Budurwar mai suna @manjaji0 ta wallafa bidiyon inda ta nuna buroshin goge hakora da safa da kuma man kai a matsayin abin da ya taba ba ta duk tsawon lokacin da suka kwashe.

Ta ce saboda bacin rai ta tattara komai na shi ta mayar masa don ba ta taba ganin mutum mai makon bala'i irin wannan saurayin nata ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel