Sojoji Sun Ceto Mutum 386 Da ’Yan Boko Haram Suka Sace Tsawon Shekaru 10

Sojoji Sun Ceto Mutum 386 Da ’Yan Boko Haram Suka Sace Tsawon Shekaru 10

  • Sojojin Najeriya sun yi nasarar ceto wasu mutanen da ‘yan ta’adda suka sace tsawon shekaru 10 zuwa yanzu
  • An bayyana sabon aikin da sojojin suka fara domin tabbatar da sun kakkabe dajin Sambisa daga masu aikata ta’addanci
  • Jihohin Arewa maso Gabas na fuskantar matsalolin da suka shafi tsaro, musamman aikin ta’addancin Boko Haram da ISWAP

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Jihar Borno - Akalla mutane 386 ne da akasari mata da kananan yara sojoji suka ceto a dajin Sambisa shekaru goma bayan sace su.

Mukaddashin GOC na shiyya ta 7 a rundunar soji, AGL Haruna ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a dajin Sambisa a karamar hukumar Konduga bayan tarbar sojojin da suka gudanar da aikin na kwanaki 10.

Kara karanta wannan

An kame satasan da suka yi amfani da bindigar sasan yara wajen Sace mota a Enugu

Sojoji sun ceto wadanda aka sace a Borno
Yadda sojoji suka ceto wadanda aka sace a Borno | Hoto: @DefenseHQ
Asali: Twitter

A cewarsa, farmakin da aka yi wa lakabi da “Operation Desert Sanity 111” an fara shi ne a aikin share dajin Sambisa daga dukkan nau’ikan ‘yan ta’adda a yankin, rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Aikin da sojoji ke yi a yanzu

Da yake jawabi, y ace:

“Kokarin da muke yi shi ne mu tabbatar da cewa mun kawar da ragowar ‘yan ta’adda a Sambisa tare da baiwa masu son tuba damar mika wuya.
“Da wannan aikin, muna sa ran da yawa daga cikinsu za su mika wuya kamar yadda suka fara.
“Mun kuma ceto wasu fararen hula; ya zuwa jiya mun ceto 386 kuma na tabbata adadin zai karu zuwa yau.”

An yabawa sojoji bisa aikin ceto ‘yan kasa

A yayin da yake yiwa sojojin bayani kan sakon babban hafsan sojin kasar, ya yaba da kwazon da suka nuna a lokacin aikin, ya kuma bukace su da su ci gaba da gudanar da aikinsu yadda ya dace.

Kara karanta wannan

An yi garkuwa da babban malamin addini a Nigeria, 'yan sanda sun magantu

Wasu daga cikin wadanda aka ceto da suka yi magana da manema labarai sun ce shekaru 10 da suka gabata aka yi garkuwa da su, Ripple Nigeria ta ruwaito.

An kame barayin mota a Enugu

A wani labarin, rundunar ‘yan sandan jihar Enugu a Kudu maso Gabashin Najeriya ta ce ta kama wasu yara maza biyu da ake zargi da laifin fashi da makami a jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Daniel Ndukwe ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a daren Juma’a 17 ga watan Mayu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel