Kotun Zabe: Hotunan Ban Dariya Yayin da Aka Gano Ganduje, Keyamo, Ozekhome Suna Likimo a Ranar Yanke Hukunci

Kotun Zabe: Hotunan Ban Dariya Yayin da Aka Gano Ganduje, Keyamo, Ozekhome Suna Likimo a Ranar Yanke Hukunci

  • A yanzu haka kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa na yanke hukunci kan kararrakin da aka shigar a kan nasarar Aswiaju Bola Tinubu
  • Kwamitin mutum biyar karkashin jagorancin Mai Shari'a Haruna Tsammani, ne za su yanke hukunci a kan zaben shugaban kasar da aka yi a ranar 25 ga watan Fabrairu
  • Sai dai kuma, bidiyoyi da hotunan da ke nuna wasu manyan yan siyasa da lauyoyi suna sharbar bacci yayin zaman kotun ya ja hankali sosai

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jama'a sun yi cece-kuce yayin da wasu hotuna da bidiyoyi suka nuna wasu manyan yan Najeriya da lauyoyi suna sharban bacci a talbijin yayin da ake zaman kotun zaben shugaban kasa a ranar Laraba, 6 ga watan Satumba.

Manyan yan siyasar Najeriya na ta sharban bacci yayin da ake zaman kotu
Kotun Zabe: Hotunan Ban Dariya Yayin da Aka Gano Ganduje, Keyamo, Ozekhome Suna Likimo a Ranar Yanke Hukunci Hoto: Channels TV, @DeborahToluwase, @thecableng
Asali: Twitter

Daga cikin wadanda aka hango suna likimo awanni bayan shiga zaman kotun akwai tsohon gwamnan jihar Kano kuma shugaban jam'iyyar All Progressives Congress na kasa (APC), Abdullahi Umar Ganduje; ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Miyagun 'Yan Fashi Sun Kai Kazamin Hari Yankuna Uku a Babban Birnin Jihar PDP

Hakazalika, an hasko gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, Lauyoyi, da yan jaridu cikin masu sharar baccin, rahoton Daily Trust.

Jama'a sun martani kan haka a soshiyal midiya

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"RAHOTO NA MUSAMMAN: BACCI, WANDA BA A CIN BASHINSA...."Kimanin awanni hudu da fara zama, mutane da dama sun yi kokarin yakar bacci amma yan tsiraru ne suka yi nasara," rahoton The Cable.

Hadimin Sanwo-Olu ya yi martani yayin da Ganduje da sauransu suke bacci a kotun zabe

Da yake martani, Jubril A. Gawat @Mr_JAGs,hadimin gwamnan jihar Lagas, Babajide Sanwo-Olu ya wallafa hotunan wadanda ke bacci a kotun zaben sannan ya rubuta a shafinsa na X:

"IDANU a kan bangaren shari'a..#Hukuncin kotun zaben shugaban kasa."

Kotun zabe ta tabbatar da nasarar Abdulmumini Jibrin Kofa

A wani labarin kuma, mun ji cewa kotun sauraron kararrakin zaben yan majalisar tarayya da ke zama a Kano ta yanke hukunci cewa Muhammad Sa'id Kiru na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ya gaza gabatar da shaidu da za su tabbatar da an tauye masa hakki a yayin zaben 2023.

Kotun zaben ta yi watsi da karar da ya shigar kan nasarar Abdulmumini Jibrin Kofa na jam'iyyar NNPP a ranar Laraba, 6 ga watan Satumba, Solacebace ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel