Jimami Yayin Da Sheikh Giro Argungu Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Jimami Yayin Da Sheikh Giro Argungu Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Al'ummar Musulmi na cikin jimami bayan samun labarin rasuwar shahararren malamin addinin Musulunci, Sheikh Giro Argungu
  • Giro Argungu ya rasu a yau Laraba 6 ga watan Satumba a Birnin Kebbi bayan fama da jinya
  • Shugaban kungiyar Izalah ta kasa, Sheikh Bala Lau da Sakatarensa Kabiru Gombe sun tabbatar da rasuwar tasa a yammacin yau

Jihar Kebbi - Shahararren malamin addinin Musulunci, Sheikh Giro Argungu ya riga mu gidan gaskiya.

Allah ya karbi rayuwar Sheikh Abubakar Giro a yammacin yau Laraba 6 ga watan Satumba.

Sheikh Giro Argungu ya rasu a Kebbi
Marigayi Sheikh Giro Argungu Ya Rasu Bayan Fama Da Jinya. Hoto: Abubakar Giro (Facebook).
Asali: Facebook

Waye ya sanar da rasuwar Sheikh Giro?

Shugaban kungiyar Izalah ta Najeriya, Sheikh Abdullahi Bala Lau shi ya bayyana haka a shafinsa na Facebook a yau Laraba 6 ga watan Satumba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Cire Tallafi: Kungiyar NLC Ta Tura Sako Ga Ma'aikata, Ta Ce An Samu Biyan Bukata

Giro kamar yadda Sheikh Kabiru Gombe ya wallafa a shafinsa na Facebook ya rasu bayan 'yar gajeriyar jinya a Birnin Kebbi.

Kabiru Gombe ya ce za a sallaci mamacin a gobe Alhamis 7 ga watan Satumba.

Yaushe za a sallaci Sheikh Giro?

Kamar yadda aka wallafa a shafinsa na Facebook za a sallaci marigayi Sheikh Abubakar Giro Argungu a gobe Alhamis 7 ga watan Satumba.

Majiyar ta ce za a yi sallar marigayin ne da misalin karfe 2:00 na rana a garin Argungu da ke jihar Kebbi.

Za a gabatar da sallar jana'izar a masallacin Idin Sarki da ke garin Argungu.

Rahotanni sun tabbatar da cewa a jiya ma kafin rashin lafiyar ta iske shi, marigayin ya yi karatu tsakanin Mangariba zuwa Isha.

Sheikh Abubakar Giro Argungu ya rasu ya na da shekaru 60 a duniya, an haifi marigayin a ranar 3 ga watan Satumba ta shekarar 1963.

Kara karanta wannan

Bidiyoyi Da Hotuna Sun Bayyana Yayin da Ganduje, Keyamo, Bala Mohammed Da Sauransu Ke Likimo a Kotun Zaben Shugaban Kasa

Giro ya bai wa addinin Musulunci gudumawa ta fannoni da dama wanda hakan ya sa ya zama daga cikin manyan malamai a kasar.

Barayi Sun Hallaka Shahararren Malamin Addini A Gombe

A wani labarin, barayi sun yi ajalin shahararren malamin addinin Musulunci mai suna Sheikh H. Musa a jihar Gombe.

Sheikh Musa wanda aka fi sani da Albanin Kuri ya rasa ransa bayan barayi sun kai masa farmaki.

Yanzu haka rundunar 'yan sanda a jihar ta bazama neman wadanda su ka aikata wannan aika-aika a birnin Gombe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel