Subul-da-baka: Sheikh Gero yayi nadamar kalaman sa kan wadanda basu son Buhari

Subul-da-baka: Sheikh Gero yayi nadamar kalaman sa kan wadanda basu son Buhari

Daya daga cikin shugabanni kuma Malaman Izala a Najeriya Shiek Abubakar Giro Argungu ya nemi afuwar 'yan Najeriya a kan wani bidiyon sa da yake nuna malamin yana kakkausan kalamai a kan "makiya" Shugaban kasar Muhammadu Buhari.

A 'yan kwanakin nan ne dai faifan bidiyon malamin ya rika yawo a kafafen sadarwar zamani inda a ciki aka ji muryar malamin yana la'antar dukkan wadanda ba su son Shugaba Muhammadu Buhari tare da yin mugunyar addu'a gare su.

Subul-da-baka: Sheikh Gero yayi nadamar kalaman sa kan wadanda basu son Buhari
Subul-da-baka: Sheikh Gero yayi nadamar kalaman sa kan wadanda basu son Buhari
Asali: Facebook

KU KARANTA: Rarara da Adam Zango sun saki sabbin wakoki kan dage zabe

Sai dai da yake tattaunawa da wakilin majiyar mu ta BBC Hausa, fitaccen malamin ya bayyana cewa bidiyon an nade shi ne tun a 2015 kuma ya yi kalaman ne sakamakon wata matsala da ta faru a siyasar wancan lokaci.

Bidiyon dai ya nuna Malamin yana kwashewa marasa goyon bayan Buhari albarka sa'annan ya yi wa marasa ci gaban Najeriya fatan hatsarin mota.

Sheik Abubakar ya ce ya yi nadamar yin wadannan kalamai kuma ya amince da kuskurensa. Malamin ya ce a wancan lokaci ya yi raddi ne ga wata kabila mai suna 'yan tatsine.

Batun shigar malaman kasar musamman ma na Izala harkokin siyasa na cigaba da jawo rarrabuwar kawuna a tsakanin mabiyan ta inda wasu ke ganin hakan bai dace ba kwata-kwata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel