Yadda Matashi Ya Rikice Hannunsa Na Rawa Yayin Duba Sakamakon Jarrabawar 'JAMB', Ya Ga Yawan Makin Da Ya Samu

Yadda Matashi Ya Rikice Hannunsa Na Rawa Yayin Duba Sakamakon Jarrabawar 'JAMB', Ya Ga Yawan Makin Da Ya Samu

  • Wani matashi ya ba mutane mamaki inda hannunsa ke rawa yayin duba sakamakon jarrabawar 'JAMB'
  • A wani faifan bidiyo, an gano matashin rike da waya ya na kokarin duba sakamakon zuciyarsa na bugawa
  • Mutane da dama sun ba shi shawara game da yadda zai a rayuwarsa bayan ganin sakamakon nashi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

A wani faifan bidiyo, an gano wani matashi na kokarin duba sakamakon jarrabawar JAMB a wayarsa a birkice hannunsa sai rawa ya ke.

Da farko ya gwada sakamakon bai nuna ba, yayin da abokansa da ke gun suka ce masa ya sake gwadawa, zuciyarsa sai bugawa ta ke.

Yadda Matashi Ya Rikice Hannunsa Na Rawa Yayin Duba Sakamakon Jarrabawar 'JAMB'
Matashin Yayin Da Ya Ke Duba Sakamakon Jarrabawar 'JAMB'. Hoto: @chancemix_1.
Asali: TikTok

Cikin rawar jiki ya sake dubawa sai ga sakamakonsa ya fito ya yi kokari ya samu maki 158, kamar yadda @chancemix_1 ya wallafa.

Ya samu maki 38 a darasin Turanci yayin ya samu maki 41 a darasin lissafi sai darasin tattalin arziki 34 da kuma darasin sanin gwamnati 45, mutane sun mai da martani cewa zai iya samun gurbin karatu a Kwalejin Fasaha.

Kara karanta wannan

Ido Zai Raina Fata: Majalisa Za Tayi Binciken Yadda Aka Saida Kadarorin Gwamnati

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ku kalli bidiyon a kasa:

Mutane sun yi martani kan bidiyon da matashin ke duba sakamakon 'JAMB'

Legit.ng ta tattaro martanin mutane game da faifan bidiyon.

Bea_kisha:

"Muna da yawa a Kwalejin Fasaha, su suke da wannan saukin mako."

WF Jerry Dc:

"Waye kuma ya tsayar da bidiyon don kallo da kyau."

vybe wrl9:

"Victor karatu ba naka ba ne."

Kelechi Mbama:

"Babu darasin da ya samu rabi."

Fortune Aluyi:

"Ka je ka koyi sana'ar hannu, ka huta da maganar makaranta."

draco:

"Ko fanta wannan maki ba zai siya ba."

Michaelson:

"Wannan aikin gona kadai za ka karantawa da shi."

Budurwa Ta Nuna Kyautar Da Saurayinta Ya Mata Tsawon Shekaru 11

A wani labarin, wata budurwa ta wallafa wani faifan bidiyo inda ta nuna kyautar da saurayinta ya mata a shekaru 11 da fara soyayyarsu.

Kara karanta wannan

An Shiga Rudani Yayin da Jami'an Amotekun Suka Halaka Wani Mahauci Dan Jihar Sokoto a Oyo

Budurwar ta ce abubuwa uku kadai ya taba ba ta kyauta tun fara soyayyarsu shekaru 11 da suka wuce inda ta ce bai yi kokari ba.

Ta nuna buroshin goge baki da safa da kuma mayin wanke kai na mata inda ta fusata ta mayar masa da kayansa har gida.

Asali: Legit.ng

Online view pixel