Jami'an Amotekun Sun Kashe Wani Mahauci Dan Jihar Sokoto a Oyo

Jami'an Amotekun Sun Kashe Wani Mahauci Dan Jihar Sokoto a Oyo

  • Jami'an tsaro na Amotekun sun kashe wani mahauci ɗan asalin jihar Sokoto a jihar Oyo
  • Mahaucin mai suna Malam Ibrahim ya rasa ran nasa ne sakamakon wata yankakkar akuya da ya sayo
  • Yan Arewa mazauna yankin sun koka kan irin cin kashin da jami'an na Amotekun ke yi musu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Oyo - Jami'an Amotekun sun kashe wani mahauci ɗan asalin jihar Sokoto mai kimanin shekaru 65, a yankin Ilora da ke karamar hukumar Afijio jihar Oyo.

Mahaukacin mai suna Malam Ibrahim, ya fito ne daga ƙaramar hukumar Wurno ta jihar Sokoto, kuma an ce ya shafe sama da shekaru 30 yana zaune da iyalansa a jihar Oyo.

Amotekun sun kashe wani mahauci dan sokoto a Oyo
Jami'an tsaro na Amotekun sun halaka wani mahauci dan jihar Sokoto a Oyo. Hoto: Oyo Affairs
Asali: Facebook

Wani abokin marigayin mai suna Aliyu Sankira Bintisau, ya shaidawa Daily Trust cewa an kashe marigayin ne ba tare da wani dalili ba.

Kara karanta wannan

Daga Karshe El-Rufai Ya Bayyana Gaskiyar Ma'anar Kalaman Da Ya Yi Kan Hanyar Da Shugaba Tinubu Ya Ci Zabe

Malam Ibrahim ya je siyan yankakkar akuya

Aliyu ya ce wani abokin kasuwancin mamacin da suka daɗe suna hulɗa ne ya kira sa domin ya zo ya sayi wata yankakkar akuya da ta sare.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce bayan marigayin ya sayi dabbar ne sai ya sanyata a cikin buhu domin ɗaukarta zuwa inda yake sana'arsa.

A cewarsa:

“A hanyarsu ta dawowa ne jami’an Amotekun suka tare su, inda Ibrahim ya yi ƙoƙarin musu bayani kan yadda aka sayo akuyar.”

Ya ce ba su bari ya gama bayanin ba sai kawai suka rufe shi da duka shi da ɗan acaɓan da ya ɗauko shi.

Jami'an sunyi yunkurin kai mamacin asibiti

Ya ƙara da cewa bayan sun masa dukan kawo wuƙa ne sai suka ɗaukesu suka je da su kasuwar inda aka tabbatar musu da cewa akuyar ba ta sata ba ce.

Kara karanta wannan

An Samu Matsala: Bene Mai Hawa Uku da Ake Tsaka Ya Aiki Ya Rushe, Bayanai Sun Fito

Aliyu ya ƙara da cewa jami'an na Amotekun sun ɗauki Ibrahim da ɗan acaɓar zuwa asibiti, sai dai Ibrahim ya cika a kan hanya.

Aliyu ya ce wannan na daga cikin irin rashin adalcin da ake yi wa 'yan arewa mazauna yankin.

Wani daga cikin abokan sana'arsa mai suna Hassan Bodinga ya ce ya san Malam Ibrahim sama da shekara 30 a wancan yankin.

Ya ƙara da cewa yara uku mamacin ya bari, biyu daga cikinsu mata ne, sai kuma namiji guda ɗaya.

An yi jana'izar wanda aka kashe bisa zargin ɓatanci a Sokoto

Legit.ng a baya ta kawo muku labarin wani mahauci mai suna Malam Usman Buba da aka kashe bisa zargin ɓatanci ga Ma'aiki (SAW) a Sokoto.

An yi masa Sallah, gami da binne shi kamar yadda akewa kowane Musulmi a ranar Talata, 27 ga watan Yuni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel