“Bayan Haihuwar Yara 4”: Matar Aure Ta Koka Yayin da Mijinta Na Shekaru 15 Ya Ce Ita Ba Ajinsa Bace

“Bayan Haihuwar Yara 4”: Matar Aure Ta Koka Yayin da Mijinta Na Shekaru 15 Ya Ce Ita Ba Ajinsa Bace

  • Wata mata yar Najeriya ta haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan ta wallafa wani abu mai tsuma rai da mijinta ya fada mata
  • Bayan shekaru 15 da aure da haifa masa yara hudu, ta ce ya fada mata cewat ita ba irin macen da yake muradi bace
  • Jama'a sun yi martani ga bidiyon nata yayin da suka karfafa ma matar da ta shiga wani hali gwiwa

Wata mata yar Najeriya ta ce mijinta ya fada mata cewar ita ba ajinsa bace bayan shekaru 15 da aurensu.

Matashiyar mai suna @star_fissy77 a TikTok, ta bayyana cewa aurensu ya samu albarkar 'ya'ya har guda hudu.

Matashiya ta koka a bidiyo
“Bayan Haihuwar Yara 4”: Matar Aure Ta Koka Yayin da Mijinta Na Shekaru 15 Ya Ce Ita Ba Ajinsa Bace Hoto: @star_fissy77
Asali: TikTok

A bidiyon na TikTok, matashiyar wacce ta karaya ta fashe da kuka yayin da take kallon kamara. Bidiyonta ya ja hankalin masu kallo fiye 117 tare da martanoni.

Masu amfani da soshiyal midiya da dama da suka kalli bidiyon sun aika ma matashiyar kalaman karfafa gwiwa, inda wasu suka caccaki mijin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

user2120011934780 ta ce:

"Kwarai da gaske bai yi karya ba saboda nan ba da jimawa ba Allah zai daukaka ki fiye da shi. Ina kaunarki yar'uwa."

babalolawaliatkeh3 ta ce:

"Dan Allah tashi, ki daina kuka, kada ki bari ya ji cewa abun ya maki ciwo, dan Allah ki fara aiki kan manufofinki, Allah madaukakin sarki ya karfafa maki zuciya sannan ya saka maki."

Deborah Adeola ta ce:

"Ki tattara wargajajjiyar rayuwarki a hannun Yesu, za ki sha mamakin yadda zai hada maki shi."

MaryK-MaaKay ta ce:

"Kuma ga ni nan ina kuka kan auren shekaru 7 ba tare da haihuwa ba wanda bai yi aiki ba...bari na huta."

nancymandy1 ta ce:

"Nan take yana cewa da ke ba ajinsa bace, sai ki fada masa cewa dama maneji kike yi da shi tun da dadewa."

Baya son 'ya'ya mata: Matar aure ta maka mijinta a kotu, ta nemi a raba su

A wani labari na daban, wata matar aure ta shigar da kara tana neman mijinta ya sake ta, bayan ya tafi ya bar su ita da yayanta guda hudu har na tsawon wata shida.

Ganiyat ta gayawa kotun kostamare ta Mapo a birnin Ibadan na jihar Oyo, cewa ba ta son ci gaba da zaman aure da Tajudeen Yaya, wanda ta zarga da rashin sauke nauyin da ke kansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel