“Kun Taba Ganin Namiji Haka?” Matashiya Ta Caccaki Masu Kiranta Da Namiji Saboda Yanayin Surar Jikinta

“Kun Taba Ganin Namiji Haka?” Matashiya Ta Caccaki Masu Kiranta Da Namiji Saboda Yanayin Surar Jikinta

  • Wata matashiyar budurwa ta haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan ta nanatawa masu shakku a kanta cewa ita din mace ce
  • A wani bidiyo da ya yadu a dandalin TikTok, matar ta yi jawabi ga mutanen da ke kin yarda cewa mace ce ita
  • A cikin wani bidiyo da ya yadu, budurwar ta ce babu gabobin namiji a jikinta sannan ta shawarci jama'a da su daina kiranta da namiji

Wata matashiya yar Najeriya ta mayar da martani ga mutanen da suka nace cewa sufar namiji ne da ita.

A cewar matashiyar mai suna @pretty_diamond777, a yanzu ba za ta iya lamuntar ci gaba da jin mutane suna yi mata lakabi da namiji ba saboda yanayin surar jikinta.

Matashiyar budurwa
“Kun Taba Ganin Namiji Haka?” Matashiya Ta Caccaki Masu Kiranta Da Namiji Saboda Yanayin Surar Jikinta Hoto: @pretty_diamond777
Asali: TikTok

Ta wallafa wani hoto da ke nuna martanin wata da suka yi ikirarin cewa ta gasa gane ainahin jinsinta.

Kara karanta wannan

“Dan Allah Ki Barni Na Sarara a Aurena”: Matashiya Ta Roki Abokiyar Sharholiyar Mijinta a Facebook, Ta Saki Hotunanta

Da take martani ga wannan, Pretty_diamond ta yi karin haske cewa ita din mace ce, ba namiji ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ta ce:

"Kun ganni kun ga wata jaraba fa. Na fada ma mutanen nan har na gaji cewa ni ba namiji bace. Ni mace ce. Bari na nuna maku. Ni mace ce. Maza na kama da wannan? Duba babu komai na nan."

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@peaceiheukwumere ta ce:

"Babu mai bin ki bashin kowani bayani, tunda dai ruwa ne ya shiga idanunsu."

@valentinalucky3 ta yi martani:

"Yarinya kada ki kula wasu mutanen Najeriya fa da wannan dabi'a tasu ta mataimakan Yesu."

@shamsuddeenbumar ya rubuta:

"Cire rigarki tukuna ina so na tabbatar da wani abu."

@norahpearl220 ta rubuta:

"Kada ki kula mutane so suke ki nuna jikinki tukuna."

@omalichanwa95 ta kara da cewa:

Kara karanta wannan

“Bayan Shekaru 15 Da Aure”: Matar Aure Ta Koka a Bidiyo Yayin da Mijinta Ya Fada Mata Ita Ba Ajinsa Bace

"Ba namiji bane mana ko dole ne."

Matar aure ta caccaki budurwar mijinta a soshiyal midiya, ta nemi ta barta ta sarara a gidan aurenta

A wani labarin kuma, wata matar aure ta koka a soshiyal midiya bayan ta zargi wata mace yar'uwarta da kokarin raba ta da farin ciki a gidan aurenta.

Matar ta kuma zargi budurwar mijin nata da daukarsa zuwa wajen wani malami wanda ya sanar da shi cewar ita ce sanadiyar matsalolin da ke damunsa a rayuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel