Bai Kyauta Ba: Dalibin Sakandare Ya Mari Kan Malaminsa, Uffan Bai Ce Ba, Bidiyon Ya Yadu

Bai Kyauta Ba: Dalibin Sakandare Ya Mari Kan Malaminsa, Uffan Bai Ce Ba, Bidiyon Ya Yadu

  • Wani malamin sakandare ya bada mamaki yayin da dalibinsa ya mari kansa amma babu abin da ya yi illa yin shiru kamar ma ba abin da ya faru
  • A wani faifan bidiyo an gano malamin yana bayani ga dalibansa don su fahimci wani abu, amma dalibin kuma hankalinsa ba ya wurin
  • Wasu daga cikin mutane da suka kalli faifan bidiyon sun dauki hakan abin dariya, yayin da wasu suka soki dalibin da rashin tarbiya

Wani dalibi dan makarantar sakandare ya jawo kace-nace a kafar sada zumunta ta zamani bayan ya mari kan malaminsa.

A wani faifan bidiyo da aka yada mai tsawon dakika 6, an gano inda malamin yake bayani ga dalibai guda biyu.

Dalibin makaranta
Dalibin Sakandare Ya Mari Kan Malaminsa, Uffan Bai Ce Ba, Bidiyon Ya Yadu. Hoto: Twitter/@instablog9ja.
Asali: Twitter

Ya na zaune da littafi a gabansa yana bayani ga daliban yayin da abin ya faru.

Faifan bidiyon ya jawo cece-kuce

Faifan bidiyon ya jawo cece-kuce a tsakanin mutane a kafar sada zumunta, kamar yadda muka gano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin da daya daga cikin daliban ya maida hankali akan abin da malamin ke fada, dayan kuma hankalinsa gaba daya akan malamin yake.

Daliban ya daura hannunsa akan malamin yana shafawa kamar yadda mai aski yake yi idan zai yi aski.

Dalibin ya sumbaci kan malaminsa

Lokacin da malamin ya gama bayani, daliban na kokarin barin wurin, a lokacin ne dalibin ya tafkawa kan malamin mari da kuma sumbatar kan malamin.

Wasu da suka kallin faifan bidiyon sun yi tsammanin ran malamin zai baci amma sai ya yi shiru, yayin da wasu suke cewa dalibin bai kyauta ba ko da kuwa malamin ya sake wa daliban na shi.

@instablog9ja ya kara wallafa faifan bidiyon

Kalli faifan bidiyon a kasa:

Mutane da dama son tofa albarkacin bakinsu akan faifan bidiyon:

@yellowwinsh:

“Idan ka yi wa malaminmu na ilimin sinadarai haka da kyar za ka nemo numfashi.”

@SheethJamaal:

“Akwai wani abu daban, amma ba a makaranta ba kam.”

@adaugo_opara:

“Wannan ya yi kama da mu’amala tsakanin uba da dansa.”

@stephen_orban:

“Irin wadannan malaman ne ke karbar kyautar gwarazan malamai na shekara, na tabbata yana da mu’amala mai kyau da dalibansa.”

@KIEMEEEEE:

“Wannan bai dace ba, dalibai ya kamata su mutunta malamansu.”

“Na Ga Rayuwa”: Musulma Yar Igbo Ta Yi Bayani, Ta Ce Tana Matukar Alfahari

A wani labarin, wata matashiya ta ce ita 'yar kabilar ibo ce kuma musulma tun lokacin haihuwarta.

A cewarta, iyayenta duka musulmai ne kuma 'yan kabilar ibo tun daga tushe, amma ta na mamakin yadda yaran da za ta haifa za su kasance.

Asali: Legit.ng

Online view pixel