“Ni Macen Aure Ce”: Budurwa Ta Sanar Da Hadadden Saurayi Yayin da Ta Yi Masa Tayin Soyayya a Bidiyo

“Ni Macen Aure Ce”: Budurwa Ta Sanar Da Hadadden Saurayi Yayin da Ta Yi Masa Tayin Soyayya a Bidiyo

  • Wata budurwa yar Najeriya ta sha kunya bayan ta yi karfin halin yi wa wani mutumin da ta gani a gidan cin abinci tayin soyayya
  • Ta isa gare shi sannan ta tallata kanta a kokarinta na shawo kan mutumin da bata taba gani ba
  • Da take bayyana kanta a matsayin macen da za a iya aura a ajiye a gida, ta fada ma mutumin cewa tana da mazauni masu kyau amma duk da haka bata samu karbuwa ba

Wata matashiyar budurwa yar Najeriya bata samu karbuwa ba bayan ta yi wa wani hadadden saurayi da ta hadu da shi a gidan abinci tayin soyayyarta.

A cewarta, ta furta soyayya ga mutumin ta hanyar fallasa sirrin zuciyarta da ke ambaton sunansa da kuma yadda ta gaza numfashi a lokacin da ta tunkaro kusa da shi.

Kara karanta wannan

“Abun da Dan Baba Yake So Kenan”: Mai Ciki Ta Farka Karfe 2:00 Na Dare Don Kona Miya, Ta Sharbi Abun ta

Matashiya cikin jama'a a wajen cin abinci
“Ni Macen Aure Ce”: Budurwa Ta Sanar Da Hadadden Saurayi Yayin da Ta Yi Masa Tayin Soyayya a Bidiyo Hoto: @ladyhephzibah
Asali: TikTok

Ta kuma sanar da shi cewa za ta kasance tare da shi duk rintsi duk wuya, amma duk wadannan bai burge mutumin ba.

Hakan bai sanyaya mata gwiwa ba inda ta kuma yin yunkuri a karo na biyu yayin da take kokarin shawo kan mutumin ta hanyar fada masa cewa ita din matar da za a ajiye a gida ce kuma ta iya girki sosai.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Matashiyar ta kara da cewar za ta iya goge-goge da yi masa duk abun da yake so, yayin da ta fada masa cewar tana da mazauna masu dan karan kyau.

Ga mamakinta, mutumin ya murmusa sannan kuma ya ki amsa tayin soyayyarta.

Bidiyonta ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

pascheers ta ce:

"Wannan na da karfin gwiwa sosai. ina son mata masu abu kai tsaye kamar ke."

Kara karanta wannan

"Samun Kwanciyar Aure Mai Kyau Ne Ya Sa Na Yi Tsawon Rai", Tsohuwa Mai Shekaru 102

ugbalaudochukwu ta ce:

"Yanzu nan kija ga mutumin kuma kina sonsa...gayen zai zata zolaya ce."

AGNI BOI ya ce:

"Ku yi kokari ku dunga aikata hakan a zahiri, mun gaji da hada-hadar kudi ta yanar gizo."

Dnice Itopa Aliyu ya ce:

"Da ciwo ko, haka abun yake a matsayin namiji."

Yadda mai ciki ta tashi tsakar dare ta kona miya, ta ce abun da dan cikinta ke so kenan

A wani labarin, wata mata mai juna biyu ta haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan ta tashi da tsakar dare don shan konannen miya.

A cewar matashiyar wacce bidiyonta ya yadu a intanet, wannan shine abun da dan cikinta ke so a lokacin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel