Garba Shehu Ya Bayyana Gaskiya Dangane Da Komawar Shugaba Buhari Nijar Bayan Ya Bar Mulki

Garba Shehu Ya Bayyana Gaskiya Dangane Da Komawar Shugaba Buhari Nijar Bayan Ya Bar Mulki

  • Garba Shehu, kakakin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya yi watsi da rahotannin cewa ƙasar Nijar za ta ba Buhari mafaka bayan ya bar ofis a ranar 29 ga watan Mayu
  • Shehu ya bayyana cewa maganar da shugaban ƙasar ya yi raha ce kawai da ya saba yi idan yana cikin matsin lamba
  • Shugaban ƙasan a ranar Talata ya bayyana cewa, ƙasar Nijar za ta ba shi kariya idan wani ya takura masa bayan ya bar ofis a ranar 29 ga watan Mayu

FCT, Abuja - Garba Shehu, mai taimakawa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, kan harkokin watsa labarai, ya yi martani kan maganar da ubangidansa ya yi cewa zai tsere zuwa Nijar idan Najeriya, ba ta ba shi kariya ba bayan ya bar ofis a ranar 29 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

Abun Hawaye: Shugaba Buhari Ya Faɗa Wa Ministoci Kalamai Masu Ratsa Zuciya A Taron Bankwana

Garba Shehu ya yi karin haske kan batun komawar Buhari Nijar
Fadar shugaban kasa ta bayyana gaskiya kan komawar shugaba Buhari Nijar Hoto: Femi Adesina
Asali: Twitter

Shehu, wanda ya bayyana hakan ne a cikin shirin Channels Television's Sunrise Daily, wanda Legit.ng ta saurara, ya ce maganar da shugaban ƙasar ya yi, kawai wata hanya ce ta zolayar da ya saba yi.

A kalamansa:

"Wannan maganar komawa Nijar ɗin nan bayan ya bar ofis, idan ka ga yadda mutane su ke ɗauke shi ta gaske, kamar cewa shugaban ƙasa ya fi son wannan ƙasar, amma zancen gaskiya ba haka abin ya ke ba. Kawai wata hanyarsa. e ta yin zolaya domin samun sauƙi idan yana cikin tashin hankali."

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ku kalli bidiyon a nan:

Kalaman Buhari sun fusata wasu ƙungiyoyi

A ranar Talata, 23 ga watan Mayun 2023, shugaba Buhari ya bayyana cewa ƙasar Nijar za ta ba shi kariya bayan ya bar mulki idan wani ya yi ƙoƙarin takura masa a Najeriya.

Kara karanta wannan

Shin Buhari Ya Canja Tunani Zai Zauna a Abuja Ya Taimaka Wa Tinubu? Ya Faɗi Gaskiya da Bakinsa

Waɗannan kalaman na shugaba Buhari, ba su yi wa ƙungiyoyin Middle Belt Forum (MBF) da Afenifere ta Yarbawa, daɗi ba inda suka caccake shi kan cewa dama bai damu da ƙasar nan ba, kuma ƴan Najeriya ba za su yi kewarsa ba idan ya bar ofis.

Nijar Za Ta Kare Ni Idan Aka Matsa Min Lamba - Buhari

A wani rahoton na daban kuma, shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa yana da kyakkyawar alaƙa da jamhuriyar Nijar.

Shugaban ƙasar ya ce idan Najeriya ta yi masa ɗumi bayan ya bar mulki, zai iya sulalewa zuwa can ƙasar abin sa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel