Hoton Khalifa Sanusi II da ‘Ya ‘yansa Mata 3 Yayin da Suka Kammala Digirgir a Landan

Hoton Khalifa Sanusi II da ‘Ya ‘yansa Mata 3 Yayin da Suka Kammala Digirgir a Landan

  • Muhammadu Sanusi II ya dauki hoto da wasu ‘ya ‘yansa mata uku da suka gama karatun digirgir
  • Hafsah (Siddika) Lamido, Shahida Sanusi da Yusra Sanusi sun samu shaidar digirgir a Landan
  • Adam S. Lamido ya ji dadin ganin cigaban da ‘yanuwansa suka samu ta bangaren ilmin zamani

Nigeria - Adam Sanusi Lamido wanda aka fi sani da Ashraf Sanusi, ya yi farin cikin kammala karatun ‘yanuwansa mata har uku.

Da yake magana a dandalin Twitter, Adam Sanusi Lamido ya nuna hotunan ‘yanuwansa bayan sun kammala karatu a jami’a.

Matashin yana mai alfahari ganin yadda Siddika Sanusi, Shahida Sanusi da Yusrah Sanusi suka samu digirgir a birnin Landan.

Ashraf Sanusi ya ke cewa ‘yanuwan na sa sun yi digirinsu na biyu ne a bangaren shari’a da tsare-tsaren jagorancin al’umma.

Sannan a ‘yanuwansa da suka kammala digirin akwai wanda ta kware a fannin ilmin nazarin Afrika, ita ce 'yar autarsu ukun.

Kara karanta wannan

Sanatoci na Barazanar Bada Umarnin Cafke Jami’in Gwamnati Kan Bacewar Miliyoyi

Adam Sanusi Lamido yana alfahari

"Ina mai alfahari da ‘yan kannai na da suka kammala digirgi a bangarorin:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Daga hagu: (Siddika) @FulaniSiddika
A tsakiya: Tsare-tsaren jagorantar al’umma (Shahida) @shayhee_LS
Daga dama: Ilmin nazarin Afrika (Yusra) @khadijasanusi_
#NewProfilePic
Khalifa Sanusi II da ‘Ya ‘yansa
Siddika Lamido, Shahida Sanusi da Yusra Sanusi Hoto: @Adam_L_Sanusi
Asali: Twitter

Ashraf Sanusi ya yi amfani da wannan hoto inda mahaifinsa yake zaune tare da 'ya 'yansa, a matsayin hotonsa a Twitter.

A Disamban nan ne aka ji ‘ya ‘yan tsohon Sarkin na Kano sun kammala karatunsu a jami’ar SOAS da ke Landan a kasar Ingila.

Martanin jama’a a Twitter

Barkansu, Allah ya sa ya amfani al’umma. A wace jami’a suka yi karatu?

- Ummar Safana

Barka ga ‘yanuwanmu.

- Shehu Na Allah

Barkansu duka. Allah ya sa ya yi amfani.

- Aminu Bala

Ina yi masu fatan alheri.

- Bala Tukur Abdullahi

Sarki Sanusi II, mai rajin ganin mata sun yi karatu.

Kara karanta wannan

Sanatan PDP Ya Ba Buhari Uzuri, Ya Fadi Inda Aka Samu Matsala a Gwamnatin APC

- B. G Mamman

Allah (SWT) ya yi masu albarka.

- MB Mai Shela

Barkansu, kuma barka ga Khalifan Tijjaniya.

- Kabir Usman Misali

Kabilancin Larabawa

A baya mun taba jin labari daya daga cikin ‘ya ‘yan tsohon Sarkin Kano, Shahida Sanusi ta zargi Larabawa da bambanci da wariyar launin fata.

Shahida Sanusi wanda take zaune a Saudi Arabiya tayi karin haske daga baya, ta ce ba za a hada Larabawa gaba dayansu, ayi masu kudin goro ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel