Sanatoci na Barazanar Bada Umarnin Cafke Jami’in Gwamnati Kan Bacewar Miliyoyi

Sanatoci na Barazanar Bada Umarnin Cafke Jami’in Gwamnati Kan Bacewar Miliyoyi

  • Kwamitin Majalisar dattawan Najeriya yana binciken kudin SWV a duk ma’aikatu da hukumomi na tarayya
  • Sanata Matthew Urhoghide ya ce suna neman Sakataren din-din na ma’aikatar tattalin arziki da kasafin kudi
  • Shugaban kwamitin ya nuna za su bukaci jami’an tsaro su kama jami’in idan ya cigaba da yi masu taurine kai

Abuja - Majalisar dattawan Najeriya tayi barazanar bada umarni a kama sakataren din-din-din na ma’aikatar tattalin arziki, tsare-tsare, kasafin kudi.

Vanguard ta rahoto cewa Sanatocin za su bukaci jami’an tsaro su sa a cafke babban jami’in idan Darekta da ma’aikatansu suka ki bayyana a gabansu.

Majalisar dattawa tana bukatar wadannan jami’ai su kawo mata wasu mmuhimman takardu da ake bukata a game da kudin da suka bace da kason SWV.

‘Yan majalisa na zargin cewa N113m sun yi kafa a wajen daidaita albashin ma’aikatan JAMB.

Kara karanta wannan

Kowa ya huta: Atiku ya fadi yadda zai yi kungiyar ASUU idan ya gaji Buhari a zaben 2023

Abin da ya sa muke barazana - Kwamiti

Shugaban kwamitin da ke binciken asusun gwamnati a majalisar dattawa, Sanata Matthew Urhoghide ya ce wannan barazanar ta zama masu dole.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Matthew Urhoghide ya shaidawa manema labarai sun dauki wannan mataki ne domin Darektan ma’aikatar tattalin arzikin ya yi ta watsi da gayyatarsu.

Sanatoci
Ahmad Lawan a Majalisa Hoto: @NgrSenate
Asali: Facebook

Jami'i ya yi kunnen-kashi

An rahoto Sanatan yana cewa kwamitinsa ya aikawa ma’aikatar takarda a ranar 20 ga watan Oktoba 2022, kuma ma’aikatan sun karbi takardar washegari.

Ana neman ma’aikatar tattalin arziki da kasafin su bada bayanin kudin da aka warewa duka ma'aikatun tarayya har da ‘yan sanda da jami’an tsaro.

Ganin bai amsa goron gayyatar ba, sai aka sake tura wata wasikar a ranar 8 ga watan Disamba 2022 a kan kudin albashin da suka bace a hukumar JAMB.

Kara karanta wannan

Elon Musk ya Saka Gadaje a Ofisoshi Twitter, Ya Ja Kunne Kan Sharholiya Babu Aiki Tukuru

Darektan kudi da gudanarwa na JAMB, Mufutau Bello ya fadawa kwamitin cewa N113m na albasin da ake magana a kai ba su shigo hannunsu ba tukun.

Duk abin da ke faruwa, kwamitin majalisar ya ba Sakataren din-din-din na ma’aikatar wa’adin sa’o’i 48 a ya zo, ko a sa jami’an tsaro su kama shi.

Zan ba Buhari 60% - La'ah

A cikin maki 100%, an samu labari cewa Sanata mai wakiltar Kudancin jihar Kaduna, Danjuma La’ah zai ba Gwamnatin Muhammadu Buhari 50% zuwa 60%.

La’ah wanda shi kadai ne Sanata daga Arewa maso yamma da ya ci zabe a PDP, yana ganin matsalar gwamnatin APC tana ga wadanda aka ba mukamai ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel