Wata Sabuwa: Jam'iyyar APC Ta Fara Shirin Tsige Gwamna Daga Kan Madafun Iko Kan Abu 1 Tal

Wata Sabuwa: Jam'iyyar APC Ta Fara Shirin Tsige Gwamna Daga Kan Madafun Iko Kan Abu 1 Tal

  • Jam'iyyar APC ta bayyana cewa ta fara duba yiwuwar tsige Gwamna Fubara na jihar Ribas kan yi wa doka hawan kawara
  • Shugaban kwamitin riƙon APC na jihar, Okocha, ya ce gwamnan ya fara wuce gona da iri wajen karya dokar kwansutushin
  • A cewarsa APC ke da mafi rinjayen mambobin majalisa dokokin jihar 27 daga cikin 32

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Rivers - Jam’iyyar All Progressives Congress (APC)  ta ce tana nazarin fara bin matakan tsige Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas kan saba wa kundin tsarin mulki.

Gwamna Fubara da Wike.
Jam'iyyar APC Ta Fara Duba Yiwuwar Tsige Gwamna Fubara na Jihar Rivers Hoto: Sim Fubara, Nyesom Wike
Asali: Facebook

Mista Tony Okocha, shugaban kwamitin riko na APC reshen jihar ne ya bayyana haka a ranar Alhamis a Abuja lokacin da yake zantawa da manema labarai.

Kara karanta wannan

Daga Ƙarshe, Gwamnan PDP ya bayyana wanda zai marawa baya a zaben mai zuwa 2024

“Ko da yake ni ba mamban majalisar dokokin jiha ba ne, amma tsige gwamna tsari ne na dimokradiyya kuma tsigewa ba juyin mulki ba ne," in ji shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Okocha ya ce jam’iyyar za ta yi duk mai yiwuwa domin kare ‘yan majalisa 27 na jam’iyyar PDP da suka sauya sheka zuwa APC, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

A kalamansa ya ce:

"Sabida haka muna faɗa wa gwamna ya shiga taitayinsa, ba zai kai labari ba idan yana take doka, zamu kai ƙorafi gaban hukumar shari'a ta ƙasa (NJC) kan umarnin da ya bayar game da mambobinmu."
"Muna kira ga jam'iyyar mu APC da ta haɗa karfi damu wajen kare 'ya'yan jam'iyya da ake cutarwa a majalisar dokokin jihar Ribas.

Wane hali yan majalisa 27 suka shiga?

Da yake magana kan rusa majalisar dokokin jihar, Okocha ya ce jam’iyyar APC ba za ta bari a ci gaba da ruguza tanade-tanaden doka ba.

Kara karanta wannan

Yanzu: Tinubu ya yi kokarin sulhu tsakanin Wike da Fubara, APC ta yi karin haske

Ya kara da cewa ‘yan majalisar da suka sauya sheka za su ci gaba da zama a wani wuri daban muddin suna tare da sandar majalisa, wadda ita ce alamar hukuma a tare da su.

Ya ce jam’iyyar APC ce ke da rinjaye a majalisar, inda ta ke da mambobi 27 cikin 32 da ke majalisar, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Karin kwamishinoni 4 sun yi murabus

A wani rahoton na daban Karin kwamishinoni huɗu sun yi murabus daga kan muƙamansu awanni bayan Antoni Janar ya yi murabus a jihar Ribas.

Wannan na zuwa ne yayin da rigima ke ƙara tsanani tsakanin gwamna mai ci, Siminalayi Fubara, da ministan Abuja, Nyesom Wike.

Asali: Legit.ng

Online view pixel