Kotu ta raba auren shekara 18 saboda mata ba ta gamsar da mijinta

Kotu ta raba auren shekara 18 saboda mata ba ta gamsar da mijinta

- Kotu ta raba aure wasu ma'aurata saboda matar tana hana mijin hakkin kwanciyar aure

- Juel Olutunji ya yi ƙorafin cewa tun bayan haihuwar ɗan su na karshe shekaru 6 da suka wuce matarsa ta ƙaurace wa shimfisarsu

- Kotu ta raba auren don a samu zaman lafiya ta kuma bawa matar rikon yara biyu mijin kuma ɗaya

Wata kotu da ke Mapo, Ibadan a ranar Juma'a ta raba auren shekara 18 tsakanin wani malami, Juel Olutunji da matarsa saboda rashin gamsuwa wurin kwanciyar aure.

Da ya yanke hukunci, Cif Ademola Odunade ya ce an raba auren saboda samun zaman lafiya tsakanin Olutunji da Blessing kamar yadda Daily Trust ta ruwaito,

DUBA WANNAN: FG ta amince za ta biya 'yan kungiyar ASUU kudin allawus N30bn

Kotu ta raba auren shekara 18 saboda mata ba ta gamsar da miji
Kotu ta raba aure. Hoto daga @daily_trust
Asali: Getty Images

Ya bawa Olutunji ikon rike yaransu biyu na farko ita kuma Blessing ya bar mata sauran yaron ɗaya.

Alƙalin ya kuma umurci Olutunji ya rika biyan Blessing N5000 duk wata a matsayin kudin abincin yaro.

Tunda farko, Olutunji ya shaidawa kotu cewa ya gaji da Blessing.

KU KARANTA: An kusa wajabtawa wa 'yan Najeriya mallakar lambar NIN - Isa Pantami

"Na shiga damuwa, bani da kwanciyar hankali saboda wasa da hankali na da matata ke yi.

"Tun lokacin da Blessing ta haifi ɗan mu na farko bayan auren mu a 2002, halayen ta suka canja ta zama fitinanniya.

"Blessing ta dena yarda dani wurin kwanciyar aure tun bayan haihuwar ɗan mu na ƙarshe shekaru bakwai da suka wuce yanzu.

"Bugu da ƙari, ta fara daukan matakan hana ni ganin ƴaƴa na," in ji Olatunji.

Blessing ba ta halarci zaman kotu ba duk da jam'in kotun ya ce an sanar da ita.

A wani labarin daban, gwamnatin tarayyar Najeriya ta umurci ma'aikatan gwamnati da ke aiki daga gida tun watan Maris saboda korona su koma aiki ranar Litinin 19 ga watan Oktoba.

Shugaban kwamitin Shugaban Ƙasa ta Yaƙi da Korona, PTF, Boss Mustapha da jagora na ƙasa, Sani Aliyu ne suka sanar da haka yayin taron manema labarai ranar Talata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel