Iyayen zamani: Iyaye sun sa dansu a gaba da fada saboda ya ki kawo budurwa gida

Iyayen zamani: Iyaye sun sa dansu a gaba da fada saboda ya ki kawo budurwa gida

  • Wani dan Najeriya yana fuskantar matsananciyar matsi daga iyayensa saboda rashin aure da rashin kawo yarinya gida tsawon shekaru
  • Iyayen sun ce dan nasu sau daya ne ya kawo wata yarinya gida, wato shekara takwas kenan, kuma tun daga lokacin ba su sake jin labarin yarinyar ba
  • Mahaifiyar mutumin da mahaifinsa sun damu sosai, sun koka cewa idan yarinya ta rabu da dansu, ya kamata wata ta shigo rayuwarsa

An ji wata uwa da uba a Najeriya suna koka damuwa matuka cewa dan su bai kawo yarinya gidansu ba tsawon shekaru takwas da suka gabata. Sun tuna a wani faifan bidiyo cewa ba a ga dan da wata yarinya ba tsawon yadda za a iya tunawa.

A wani faifan bidiyo da @instablog9ja ya wallafa a Instagram, an ga dan yana zaune dirsham yana jin iyayensa cikin nutsuwa. Mahaifiyar ce ke magana yayin da uban ya amince da wasu 'yan kalamanta.

Kara karanta wannan

Ko shaiɗan ba zai faɗi abubuwan da ake yaɗawa ba, Mummy GO ta ce lalata bidiyoyin ta aka yi

Dan Najeriya ya sha fada saboda ya ki aure
Iyayen zamani: Iyaye sun sa dansu a gaba da fada saboda ya ki kawo budurwa gida | Hoto: @instablog9ja and Birgit Korber / EyeEm
Asali: Instagram

Iyayen sun ce idan yarinyar ta rabu dashi, daidai ne saurayin ya nemi wata. An ji mahaifiyar tana cewa:

"Duk tsawon shekarun nan ba ka yi ba. Ban sani ba. Domin a rayuwata sau daya kacal ya kawo wata yarinya cin abincin gidanmu, sau daya kawai. Bayan haka, ba zan iya yanke wani abu daga wannan ba. Ba zan iya ba. Eh yana son mutane daga Najeriya, watakila yana son doguwa gajera, a tsaka-tsaki masu ilimi, ba ni da masaniya saboda abu daya ne kawai ya faru, bai tabbata ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Idan wata ta tafi wata ya kamata ta zo, ba za ka cemin ka yi soyayya da wata kusan shekaru takwas da suka wuce ba, kuma daga wancan lokaci zuwa yanzu, babu wata wacce ta dace ka kawo gida cin abinci, akwai dai wata matsalar. Shine kawai!"

Kara karanta wannan

Gombe: Mai adaidaita sahu ya yi garkuwa da kansa don ya samu N500,000 ya biya bashin da 'yar uwarsa ke binsa

Kalli bidiyon:

'Yan Najeriya a shafin Instagram sun caccaka tsinke

'Yan Najeriya a shin Instagram sun yi sharhin ban dariya game da bidiyon yadda iyayen ke sa dansu a gaba.

Ga kadan daga cikin sharhin:

@nellynells__:

"Muna da yawa don wannan dandali na WhatsApp."

@adeoluolatomide:

"Dan dakata, nan kusa za su kawo maka mata."

@itisugochukwu:

"Kayi sa'a da basu daura maka aure da wata ba daga kauye."

@audrey_mula:

"Hakika iyayenmu ba su fahimci gwagwarmayar ba. Muna son gabatar muku da mace daya kacal kuma lokacin da wannan matar --- dole ne mu tabbatar da cewa ba za mu sake maimaita kuskure ba."

@ethanojogan:

"Dole iyayen Najeriya suna da makarantar sirri da suke zuwa a wani wuri."

A wani labarin kuwa, wani ango ya bayyana aniyarsa na kawo karshen auren da ke tsakaninsa da matarsa kan zargin da ya shiga tsakani.

Labarin da aka yada ya nuna cewa mutumin ya kama matarsa tana sheke ayarta da wani kato kwanaki kadan bayan aurensu.

Kara karanta wannan

Ina fatan na sake ganinsa: Inji attajirin mahaifin Abdul Mutallab, wanda aka kama da bam a Amurka

A cewar labarin da @chuddyOzil ya wallafa a shafinsa na Twitter, mutumin da matarsa sun yi aure ne a ranar 27 ga watan Disamba, 2021. Sai dai rikicin ya soma ne lokacin da mutumin ya kama matarsa da wani mutum a wurin da suke shakatawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel