Cin amana: Ango ya kama amaryarsa da kwarto bayan kwana 9 da aurensu

Cin amana: Ango ya kama amaryarsa da kwarto bayan kwana 9 da aurensu

  • Wani dan Najeriya na shirin sakin sabuwar amaryarsa bayan ya gano tana sheke ayarta da wani bayan aurensu
  • Daurin auren ya cika kwana 9 kenan, amma tuni mutumin ya shirya mai yiyuwa don ganin matar ta bar gidansa
  • Mutumin ya ce ya kama sabuwar amaryar tasa da wani mutum kato a wani wurin da yace sam bai masa ba

Wani ango ya bayyana aniyarsa na kawo karshen auren da ke tsakaninsa da matarsa kan zargin da ya shiga tsakani.

Labarin da aka yada ya nuna cewa mutumin ya kama matarsa tana sheke ayarta da wani kato kwanaki kadan bayan aurensu.

Aure zai mutu bayan rikici
Sai na sake ta: An go ya shiga tashin hankali yayin da kama matarsa da kwarto kwana 9 bayan aurensu | Hoto: @chuddyOzil and Ana Maria Serrano
Asali: Twitter

A cewar labarin da @chuddyOzil ya wallafa a shafinsa na Twitter, mutumin da matarsa sun yi aure ne a ranar 27 ga watan Disamba, 2021. Sai dai rikicin ya soma ne lokacin da mutumin ya kama matarsa da wani mutum a wurin da suke shakatawa.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan sanda sun shiga tsakani yayin da kwarto ya kashe mijin daduronsa

Labarin ya ce ana daukar matakan kawo karshen auren nan kusa:

A cewar rubutun na Twitter:

"An yi aure (gargajiya da coci) a ranar 27 ga Disamba, 2022, an kama ta tare da daya daga cikin samarinta a ranar 5 ga Janairu 2021, suna luguden lebe a kwalbar giya a cikin wani yanayi na dadi. Mijin da umunna sun riga sun shirya bin hanyar al'ada. Aure ya kare!"

'Yan Najeriya a shafin Twitter sun mayar da martani yayin da wani mutum ke shirin sakin matarsa bayan kwana 9 da aure

Labarin ya haifar da zazzafan martani daga ’yan Najeriya a dandalin Twitter.

Wata mata wacce ta yi rubutu da sunan @judithsweetest ta ambaci cewa ta ga irin wannan lamari.

Ta ce:

"Na ga irin wannan shari'ar. Mutumin ya kwana da wata a wani otal kwana daya kafin bikin aurensa, sai wani ya sanar da matar da zai aura saboda gobe za a yi bikinsu mai tsarki."

Kara karanta wannan

Yadda magidanci ya kashe matarsa da duka bayan sun samu sabani a Nasarawa

Wasu masu martani a kan rubutunta sun yi nasu batun kamar haka:

@nonsookongwu1:

“Auren ya samu rusasshen tushe, ko dai saurayin bai san matar ba ko kuma an tilasta mata auren saurayin, mun ga auren da ya girma ya yi karfi, menene duk wadannan batutuwa na cewa aure ya zama abin ban tsoro."

@doyin_deji:

"...Me mutane ke so ne kam? Idan basu yi aure ba sai su yi ta korafi, kuma idan sun yi aure sai su yi ta ha'inci. Me yasa mutane ke da wuyar sha'ani wajen biyayya ga abokan zamansu?

@XerxesEmperor

“Idan muka juya jinsin, a kasar nan Najeriya, wannan labarin ba zai kare a kashe aure ba, Fastonta, Fastonsa, ‘yan uwansa da abokansa na arziki, wasu ‘yan uwanta da abokanta na arziki, duk za su taru su ce ta yafe masa. zai canza."

Yayin da wata ke ha'intar aure, wata Amarya mai suna, Fatima Balarabe Haruna, ta riga mu gidan gaskiya kwanaki 35 da fara sabuwar rayuwar aure a dakin mijinta a jihar Kano.

Kara karanta wannan

Wani mutum ya dawo daga kasar waje, ya tarar wani yana gina katafaren gida a filinsa, mutane sun magantu

Mahaifin marigayiya Fatima, Balarabe A Haruna, shi ne ya sanar da rasuwar diyarsa a dandalin sada zumunta Facebook.

Yace an daura auren Fatima Balarabe a ranar 4 ga watan Disamba, 2021, wata daya da kwana biyar kenan kuma Allah ya karbi abinsa.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel