Ko shaiɗan ba zai faɗi abubuwan da ake yaɗawa ba, Mummy GO ta ce lalata bidiyoyin ta aka yi

Ko shaiɗan ba zai faɗi abubuwan da ake yaɗawa ba, Mummy GO ta ce lalata bidiyoyin ta aka yi

  • Fitacciyar fasto, Funmilayo Adebayo, wacce ta yi suna a kwanakin nan wurin hankada mutane wuta, ta ce wasu daga cikin bidiyoyinta duk lalata su aka yi
  • Wacce aka fi sani da Mummy GO, ta ce babu shakka wasu daga cikin kalaman da ake lakaba mata, ko shaidan ba zai fade su ba idan zai yi wa'azi
  • Sai dai kuma, ta ce kalamanta duk daga bibul suke, masu lalata bidiyoyin kuwa suna yi ne domin nishadi, wanda tace ba ta ji haushin haka ba

Funmilayo Adebayo, fitacciyar faston Najeriya wacce aka lakaba wa suna Mummy GO, ta yi ikirarin cewa bidiyoyin da ake yadawa kan da'awarta na hankada mutane wuta duk shirya su aka yi.

Mummy GO ta zama abun magana a kafafen sada zumunta kan yadda wa'azin ta da da'awoyin ta ke hankada mutane wuta kai tsaye.

Kara karanta wannan

Obasanjo ya bayyana hanyar magance rashin aikin yi ga matasan Najeriya

A tattunawar faston da BBC, ta yi magana kan yadda ake yin martani daban-daban kan koyarwarta.

Ko shaiɗan ba zai faɗi abubuwan da ake yaɗawa ba, Mummy GO ta ce lalata bidiyoyin ta aka yi
Ko shaiɗan ba zai faɗi abubuwan da ake yaɗawa ba, Mummy GO ta ce lalata bidiyoyin ta aka yi. Hot daga thecable.ng
Asali: UGC

Ta ce ko shaidan dai ba zai yi wasu daga cikin tsokacin da ake alakantawa da ita ba a kafafen sada zumunta.

"Na ga wasu daga cikin bidiyoyin amma ban ji haushi ba saboda duk masu wallafar nan babu makiyana. Kashi casa'in daga cikinsu suna yi ne domin nishadi a kafafen sada zumunta. Basu san ni ba," tace.
"Wasu basu san dalilin da yasa aka fara ba. A Najeriya, matsala ta yi wa matasa yawa. Mutane suna bukatar nishadi. Wasu basu san ina rayuwa ba. Ban fadi wasu daga cikin abubuwan nan ba. Dukkan bidiyoyn hada su aka yi.
"Ko shaidan ba zai fadi wasu abubuwan ba idan da zai zama fasto ballantana kuma mai da'awa. Wadanda ke yin hakan sun fara kusan shekaru takwas da suka gabata. Sun fara da mujallu ne amma sai suka fara aiko masu makamai domin su kawo min farmaki, hakan bai yi aiki ba.

Kara karanta wannan

Rikici: Mata ta kai karar TikTok saboda samun matsalar kwakwalwa tsabar kallo a kafar TikTok

"Dukkan da'awa ta daga bibul nake samowa. Ina ta samun wayoyin mutane, Funmi, kina da tasiri a kanmu. Wasu daga cikin mambobin cocinmu tserewa suke yi. Idan ba ki daina ba za mu kashe ki," na yi tunanin barazana ce kawai.
"Mutane sun fara kai min farmaki da bindigogi. Suna barazana ga rayuwata amma ban sauya ba. Toh hakan yasa suka fara amfani da soshiyal midiya. Idan sun ce da'awata na da zafi, idan sun ce kalaman Ubangiji na da tsauri, su bar tsirarun mutanen da ke bi na su kiyaye."

Kungiya ga Ortom: Ka mayar da hankali wurin biyan albashi a Benue, maimakon matsawa Buhari

A wani labari na daban, kungiyar matasan Tiv ta fadin duniya ta yi kira ga gwamna Samuel Ortom na jihar Benue da ya mayar da hankali wurin dawo da sunansa da bunkasa walwalar ma'aikata a jihar fiye da "amfani da sunan shugaban kasa Muhammadu Buhari a kanun labarai".

Kara karanta wannan

Ikon Allah: Yadda raken N50 ya jawo rikicin da ya kai ga zub da jini da garkame kasuwa a jihar Kwara

Shugaban kungiyar matasan Tiv, Honarabul Mike Msuaan, ya fadi hakan ne yayin mayar da martani ga amsar da Ortom ya bawa shugaban kasa Muhammadu Buhari bayan tattaunawa da ChannelsTV.

Daily Trust ta ruwaito cewa, sanannen abu ne cewa gwamna Ortom ya kawo wa jihar Benue ci bayan shekara 20 sannan ya zama kadangaren bakin tulu ga cigaban jihar, kungiyar tace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel