Rudani: Hisbah ta ce babu batun gayyatar iyayen sarauniyar kyau Shatu Garko, ta yi bayani

Rudani: Hisbah ta ce babu batun gayyatar iyayen sarauniyar kyau Shatu Garko, ta yi bayani

  • Hukumar Hisbah a jihar Kano ta magantu kan cewa ta gayyaci iyayen Shatu Garko, sarauniyar kyau ta Najeriya
  • Wannan na zuwa ne bayan da kwamandan hukumar ya bayyana yiyuwar gayyatar iyayenta domin su tattauna
  • Kafafen sada zumunta sun cika da bayanai kan wannan lamari, amma Hisbah ta musanta gayyatar iyayen Shatu Garko

Kano - Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta yi watsi da furucin da ta yi a baya na gayyatar sarauniyar kyau, Shatu Garko da iyayenta domin amsa tambayoyi a ofishinta.

Gidan radiyon Freedom da ke Kano ya bayyana cewa, ya tattauna da Babban Daraktan Hukumar Hisbah ta Kano Dr. Aliyu Musa Aliyu Kibiya kuma ya ce lallai babu wannan batu.

Sarauniyar Kyau ta 44, Shatu Garko
Rudani: Hisbah ta ce bata gayyaci iyayen sarauniyar kyau Shatu Garko ba, ta yi bayani | Hoto: @shatu.garko
Asali: Instagram

A cewar Kibiya, tambayar Sheikh Ibn Sina aka yi kan batun, shi kuwa ya bayyana nasiharsa ga iyayenta da kuma daukacin alumma.

Kara karanta wannan

Sarauniyar kyau: 'Yan Najeriya sun caccaki Hisbah kan yunkurin gayyatar iyayen Shatu Garko

A wata tattaunawa da ya yi da jaridar Sahelian Times, Kakakin Hukumar, Lawan Ibrahim Fagge, ya bayyana cewa bai san wani shiri na gayyatar Shatu Garko ko ‘yan uwanta ba.

A kalamansa:

"Na samu kira daga 'yan jarida a kokarinsu na tabbatar da sahihancin labaran da kafafen yada labarai daban-daban suka yada.
"Abin takaici, Kwamandan Hukumar bai kasance a ofis ba jiya kuma bai zauna a yau ba."

Idan baku manta ba, Legit.ng Hausa ta kawo rahoto a baya cewa, kwamandan Hisbah, Ibn Sina ya ce sam Hisbah bata amince da abin da Shatu Garko ta aikata ba, inda ya ce hukumar za ta gayyaci iyayenta don su tattauna batun.

A kalamansa:

"Mu (Hisbah) ba mu yarda cewa Shatu Garko 'yar Musulmai bace 'yar jihar Kano da iyayenta suka fito daga karamar hukumar Garko ba, Kano kasar Shari'a ce, kuma dalilin da ya sa ba za mu yarda lamarin ya tafi haka kawai ba kenan."

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Hisbah a Kano ta ce dole ta zauna iyayen sarauniyar kyau Shatu Garko

“Za mu gayyaci iyayenta mu tattauna da su game da abin da ‘yarsu ta aikata da kuma cewa abin da ta yi haramun ne a Musulunci. Wannan kenan don su san cewa ba za ta ci gaba da bin wannan hanyar ba, sannan ta hana sauran ‘yan matan bin sahunta.”

Sai dai, wadannan batutuwa na Hisbah basu yi wa jama'a da dama dadi ba, inda da dama suka tofa albarkacin bakinsu.

Gashi yanzu kuma, Hisbah ta ce sam babu batun, Ibn Sina bai fada ba.

Sanata Shehu Sani ya yi martani ga Hisbah kan batun gayyatar iyayen sarauniyar kyau, Shatu Garko

A bangare guda, Sanata Shehu Sani ya ce ya kamata a jinjinawa sarauniyar kyau wato Miss Nigeria ta 44, Shatu Garko, da ta lashe gasar duk da tana sanye da hijabi.

Tsohon majalisar da ke wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar wakilai ta takwas, ya ce da samun nasarar ta sanye da hijabi, Shatu Garko “ta tabbatar da akwai kyawu da kawa a cikin kamun kai."

Kara karanta wannan

Sabbin zafafan hotunan Shatu Garko, sarauniyar kyau ta Najeriya da suka girgiza Instagram

Ya kara da cewa budurwar "ta yi nasara ga duk wadanda ba su yarda cewa kyau na nufin tsiraici ba."

Asali: Legit.ng

Online view pixel