Wata sabuwa: Hisbah a Kano ta ce dole ta zauna iyayen sarauniyar kyau Shatu Garko

Wata sabuwa: Hisbah a Kano ta ce dole ta zauna iyayen sarauniyar kyau Shatu Garko

  • Hisbah a jihar Kano ta ce za ta gayyaci iyayen sabuwar sarauniyar kyau da aka zaba na wannan shekarar saboda su magantu
  • Hisbah ta ce sam abin da ta aikata ba daidai bane, kuma dole a zauna akai a san mafita da kuma gano hanya a gaba
  • Kwamandan Hisbah ne ya bayyana haka a wata hira da yayi da gidan labarai bayan nada Shatu Garko a matsayin Miss Nigeria

Kano - Kwamandan rundunar Hisbah ta jihar Kano, Sheikh Haruna Ibn Sina, ya ce za su gayyaci iyayen sarauniyar kyau, Shatu Garko domin su magantu game da rawar da ta taka.

Matashiyar ‘yar shekara 18 ta samu nasarar lashe gasar zakarun mata ta Miss Nigeria karo na 44 a ranar 17 ga Disamba, 2021 kuma ta kasance mace mai sanya hijabi ta farko da ta lashe gasar.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Ware Makudan Miliyoyi, Ya Tallafawa Mutanen da Ambaliya Ta Shafa a Kano

Sarauniyar kyau Shatu Garko
Wata sabuwa: Hisbah a Kano ta ce dole ta zauna iyayen sarauniyar kyau Shatu Garko | Hoto: @shatu.garko
Asali: Instagram

Hisbah ta ce dalilin da ya sa za ta gayyaci iyayen kawai domin su gaya musu cewa Musulunci ya haramta wa diyar tasu shiga gasar kyau ne.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewar Hisbah ga BBC Pidgin:

"Mu (Hisbah) ba mu yarda cewa Shatu Garko 'yar Musulmai bace 'yar jihar Kano da iyayenta suka fito daga karamar hukumar Garko ba, Kano kasar Shari'a ce, kuma dalilin da ya sa ba za mu yarda lamarin ya tafi haka kawai ba kenan."

Hakazalika, zaman zai bayyanawa iyayenta haramcin shiga gasar da kuma hana ta anan gaba kana da zama izina ga 'yan baya.

Hisbah ta ce AlQur'ani ya haramta shiga gasar kyau.

Sheikh Ibn Sina, wanda fitaccen malamin addinin Musulunci ne kafin a nada shi a matsayin shugaban Hisbah ya karanto wasu ayoyi daga AlQur'ani da kuma kawo bayanai na addini kan haramcin gasar.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Mataimakiyar Kakakin APC Ya Bayyana Jihohin Arewa Da Obi Zai Iya Cin Zabe

Hakazalika, ya kawo maganganun magabata a tarihin musulunci da suka yi Allah wadai da wannan dabi'a ta shiga gasar kyau.

Ya kuma yi tsokaci kan yadda gasar ta ke ingiza mata zuwa sanya tufafi mai nuna tsiraici, lamarin da yace haramun ne a Musulunci.

A cewarsa, Allah ya ce:

"Allah Madaukakin Sarki ya ce wa Annabi ya gaya wa matansa, 'ya'ya mata da mata masu imani su suturta jikinsu da kyau."

A bayanansa ya kuma yi nuni da irin kwalliya da kuma inda aka halastawa mace ta nuna a jikinta.

Kwamandan ya kuma kara da cewa masu shirya gasar suna son jawo fushin Allah ne saboda abu ne da ya so.

A baya kun ji cewa, a ranar Asabar ne labari ya karade kafafen watsa labaran Najeriya kan sanar da wata 'yar jihar Kano, Shatu Garko a matsayin sarauniyar kyau ta Najeriya.

Shatu Garko ‘yar shekaru 18 da haifuwa da ake kallo da Hijabi ta ciri tuta a gasar kyau ta Miss Nigeria karo na 44 wannan shekara ta 2021.

Kara karanta wannan

Kamfen 2023: Tinubu ya yi magana mai girma game da bashin da ake bin Najeriya

An nada ta a matsayin sarauniya ta 44 ne a gasar a lokacin tantacewar karshe na gasar da aka gudanar a Legas a daren Juma’a, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Kyakkyawar budurwa 'yar Kano ya ciri tuta

A tun farko, kyakkyawar budurwa 'yar Arewa maso yammacin Najeriya, Shatu Garko, ta lashe gasar Mace mafi kyau a Najeriya watau 'Miss Nigeria' na shekarar 2021.

Shatu Garko, yar shekaru 18 kacal ce mace mai Hijabi daya tilo cikin dukka sauran yan takaran gasar.

Adebimpe Olajiga ta bayyana hotunan bikin yayinda ake karrama Shatu bayan nasarar da tayi a gasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel