Sanata Shehu Sani ya yi martani ga Hisbah kan batun gayyatar iyayen sarauniyar kyau, Shatu Garko

Sanata Shehu Sani ya yi martani ga Hisbah kan batun gayyatar iyayen sarauniyar kyau, Shatu Garko

  • Sanata Shehu Sani ya yi Allah-wadai da matakin da hukumar Hisbah ta dauka na gayyatar iyayen Shatu Garko kan fitowar ‘yarsu a matsayin sarauniyar kyau
  • Tsohon dan majalisan ya ce kamata ya yi a jinjina wa Shatu Garko da ta lashe gasar Miss Nigeria duk da kuwa tana sanye da hijabin ta
  • A cewar Sani, sabuwar Miss Nigeria da ta yi nasara duk da kasancewarta mai hijabi ya tabbatar da cewa akwai kyau da kawa a cikin ladabi da kamun kai

Kaduna - Sanata Shehu Sani ya ce ya kamata a jinjinawa sarauniyar kyau wato Miss Nigeria ta 44, Shatu Garko, da ta lashe gasar duk da tana sanye da hijabi.

Tsohon majalisar da ke wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar wakilai ta takwas, ya ce da samun nasarar ta sanye da hijabi, Shatu Garko “ta tabbatar da akwai kyawu da kawa a cikin kamun kai."

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Hisbah a Kano ta ce dole ta zauna iyayen sarauniyar kyau Shatu Garko

Ya kara da cewa budurwar "ta yi nasara ga duk wadanda ba su yarda cewa kyau na nufin tsiraici ba."

Sarauniyar Kyau ta 44, Shatu Garko
Sanata Shehu Sani ya yi martani ga Hisbah kan batun gayyatar iyayen sarauniyar kyau | Hoto: @shatu.garko
Asali: Instagram

A kalaman Sanata Sani a wani sakon da ya wallafa a Facebook a ranar Laraba, 22 ga watan Disamba, ya ce:

“Malama Shatu Garko ta saka hijabi ta yi nasara, ta tabbatar da akwai kyau da kawa cikin kamun kai, ta karyata kasuwar batsa, ta taka rawa cikin mutunci da karimci, ta bijire wa rashin daidaito, cin zarafi da al'adar da aka saba da ita sannan ta daga kofin nasara, ita ce abar koyi da ya kamata a kwaikwaya, ba wai ga gasar kyau ko kyan gani ba.
"Ta yi nasara ne ga duk wanda bai yarda cewa kyau shi ne tsiraici ba. Ta samu nasara ga duk masu sanya hijabi irinta. Ya kamata masu tsarkinmu su yaba mata saboda ta dauki wata hanya ta daban ko wacce ba a saba gani ba kuma ta samu nasara."

Kara karanta wannan

Sabbin zafafan hotunan Shatu Garko, sarauniyar kyau ta Najeriya da suka girgiza Instagram

Tarihi dai ya rubuta cewa, Shatu Garko ita ce mai hijabi ta farko da ta lashe kambin sarauniyar kyau na Miss Nigeria tun lokacin da aka fara gasar kyau a kasar.

Legit.ng ta fahimci cewa, Shehu Sani ya yi wannan tsokaci ne a daidai lokacin da hukumar Hibah ta jihar Kano ta bayyana shirin gayyatar iyayen Shatu Garko don su tattauna batun.

Hisbah a Kano ta ce dole ta zauna da iyayen sarauniyar kyau Shatu Garko

A tun farko, kwamandan rundunar Hisbah ta jihar Kano, Sheikh Haruna Ibn Sina, ya ce za su gayyaci iyayen sarauniyar kyau, Shatu Garko domin su magantu game da rawar da ta taka.

Matashiyar ‘yar shekara 18 ta samu nasarar lashe gasar zakarun mata ta Miss Nigeria karo na 44 a ranar 17 ga Disamba, 2021 kuma ta kasance mace mai sanya hijabi ta farko da ta lashe gasar.

Kara karanta wannan

Wata soja ta gamu da fushin gidan soja yayin da ta amince za ta auri dan bautar kasa

Hisbah ta ce dalilin da ya sa za ta gayyaci iyayen kawai domin su gaya musu cewa Musulunci ya haramta wa diyar tasu shiga gasar kyau ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel