Sarauniyar kyau: 'Yan Najeriya sun caccaki Hisbah kan yunkurin gayyatar iyayen Shatu Garko

Sarauniyar kyau: 'Yan Najeriya sun caccaki Hisbah kan yunkurin gayyatar iyayen Shatu Garko

  • Hukumar Hisbah tana shan caccaka bayan batun shirinta na gayyatar iyayen Shatu Garko, wacce ta lashe gasar sarauniyar kyau a 2021
  • Garko, ita ce mace ta farko daga jihar Kano da ta lashe gasar wacce aka yi a jihar Legas a daren Juma’ar da ta gabata
  • Sai dai bayan hira da manema labarai, inda kwamandan Hisbah, Harun Ibn Sina, ya ce zasu gayyaci iyayenta, mutane sun yi ta sukar hukumar

Kano - Hukumar Hisbah reshen jihar Kano ta na shan caccaka bayan bayyana shirin ta na gayyatar iyayen Shatu Garko, wacce ta lashe gasar sarauniyar kyau a 2021.

Garko mai shekaru 18 wacce ta zama mace ta farko mai Hijabi daga jihar Kano ta lashe gasar wacce aka yi a ranar Juma’a da dare a jihar Legas, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Hisbah a Kano ta ce dole ta zauna iyayen sarauniyar kyau Shatu Garko

Sarauniyar kyau: 'Yan Najeriya sun caccaki Hisbah kan yunkurin gayyatar iyayen Shatu Garko
Sarauniyar kyau: 'Yan Najeriya sun caccaki Hisbah kan yunkurin gayyatar iyayen Shatu Garko. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Sai dai kwamandan Hisbah, Harun Ibn Sina, ya sanar da Daily Trust cewa gasar sarauniyar kyau ta ci karo da koyarwar addinin islama.

Ya karanto ayyoyi daga Al-Qur’ani mai girma da su ka ci karo da abinda Garko ta yi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamar yadda yace:

“Mun yi bincike kuma mun gano cewa ‘yar asalin jihar Kano ce kuma ‘yar karamar hukumar Garko ce.
“A musulunce duk abinda ta yi ya ci karo da koyarwar addinin musulunci kuma ba hali mai kyau bane. A musulunci bai dace mace ta bayyana surar jikin ta ga wani ba face mijinta, yaranta ko ‘yan uwanta. Don haka ba za mu lamunci wannan mummunar dabi’ar ba.”

Ya ce zasu gayyaci iyayenta akan wannan abu da diyarsu ta aikata.

Saidai bayan tuntubar jami’ar kare hakkin bil adama ta CHRICED, Zuwaira Umar, ta ce wannan abinda Hisbah ke shirin yi shiga hakkin bil’adama ne.

Kara karanta wannan

Sabbin zafafan hotunan Shatu Garko, sarauniyar kyau ta Najeriya da suka girgiza Instagram

Kamar yadda tace:

“Tana da damar yin abinda ta ga dama kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya bata damar. Babu wata doka a Kano da ta ke hani ga munanan ayyuka, abinda ta yi bai kai wanda yaran masu kudi suke yi ba, amma hukumar bata taba hukunta su ba.
“Diyar yaran masu kudi a Kano ta yi shigar da ta fi ta Shatu Garko muni amma babu abinda aka yi. Sannan ba a Kano ta yi ba, don ba a Kanon take zama ba.”

Ta kara da cewa ba a zabar sarauniyar kyau don kyau kadai, har da ilimi da sauran abubuwa.

Shehu Sani, tsohon sanata ya yi magana dangane da lamarin, hakan ya janyo cece-kuce a kafafen sada zumunta.

Kamar yadda ya wallafa a Twitter:

“Ms Shatu Garko ta yi takarar sarauniyar kyau da shiga mai kyau. Bata saba wa al’adunmu na arewa ba. Akwai yaran masu kudi da mulki da su ka yi munanan abubuwa da dama. Ina bukatar ‘yan Hisbah su sakar mata mara ta yi fitsari.”

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da 'yan bindiga sun sace sarkin gargajiya da malamin fada

A bangaren Aisha Yesufu, ‘yar gwagwarmaya, cewa tayi:

“Don diyata ta yi takarar sarauniyar kyau sai a gayyace ni? Kai! A ranar zasu san cewa mun cancanci gado a asibitin mahaukata. Shirmen banza da na wofi! Kalli wani shashanci da rashin wayau!”

Gimba Kakanda a bangarensa cewa yayi:

“Ina ganin Hisbah su na jin dadin cin zarafin musulmai musamman na arewa. Ban ga amfanin gayyatar iyayen Shatu Garko ba. Akwai matsaloli da dama da suke addabar al’ummar musulmai amma ba su mayar da hankali ba sai kan na yarinya karama da ta nemi sarauniyar kyau.”

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel