Latest
Tsohon sakataren gwamnati, Babachir Lawal ya ce Shugaba Bola Tinubu na cikin ruɗani saboda haɗakar adawa da Atiku Abubakar da Nasir El-Rufai ke jagoranta.
An shiga jimami a jihar Plateau bayan samun labarin rasuwar tsohon mataimakin gwamnan jihar, Farfesa Sonni Gwanle Tyoden. Ya rasu ne a ranar Lahadi, 4 ga watan Mayu.
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya karyata zargin da Dr Abdullahi Baffa Bichi ya yi na cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na karbar 2bn a kudin Kano duk wata.
Jam'iyyar APC ta sake samun ƙarfi bayan tsohon na hannun daman Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya sauya sheka tare da wasu tsofaffin mambobin PDP a Kano.
Mutane sun shiga mamaki bayan sace Fasto John Okoriko ya ce babu wani wurin da ake kira aljanna ko wuta, yana mai cewa Allah na kasancewa a zuciyar mai bi.
Mele Kyari, tsohon shugaban NNPCL ya bayyana cewa, ba a kama shi ba, kuma yana nan yana hutawa a gida. Ya bayyana cewa, ya kamata a daina yada jita-jita.
An samu asarar rayuka bayan mafarauta sun gwabza fada da 'yan bindiga a jihar Sokoto. 'Yan bindigan sun kuma yi barna bayan sun kai wani hari a cikin kauye.
Ana ta kokarin sulhu da Siminalayi Fubara, rikici ya sake kunno kai a jihar Rivers yayin da yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Gwamnn da Nyesom Wike ta rushe.
An zauna da Wike domin tabbatar da an dinke duk wata baraka gabanin zaben 2027 da ke tafe nan ba da dadewa ba. APC na ci gaba da karbar manyan jiga-jigan PDP.
Masu zafi
Samu kari