Latest
An bayyana adadin kujerun majalisar wakilai da jam'iyyar APC ta samu a zaben da aka kammala na cike gurbi a ranar Asabar 15 ga watan Afrilun wannan shekarar.
Shugaba Buhari ya nuna takaicin sa kan rikicin da ya ɓarke a ƙasar Sudan, shugaban ƙasar ya yi kiran da ɓangarorin biyu da su tsagaita wuta su hau teburin sulhu
A yau aka taka wasan karshe a zabukan da INEC ta ce ba su kammalu ba a faɗin kasar nan, mun tara muku sakamakon zaben daga jihohin Katsina, Kaduna da Zamfara.
Bayan kammala zaben cike gurbi, an fadi adadin kujerun da aka sanar na majalisar dattawa a Najeriya. A halin da ake ciki, APC ce ke da mafi rinjayen sanatoci.
Rahotanni sun tabbatar da ɓarkewar rikici a ƙaramar hukumar Bogoro ta jihar Bauchi kan naɗin sarautar basaraken ƙauyen Kang na ƙaramar hukumar. Rai ya salwanta.
Rahoto ya ce Aisha Binani ta lashe zabe, amma hukumar zabe ta INEC ta ce sam hakan bai yiwu ba. Mun kawo muku bayanai game da zababbiyar gwamnan jihar Adamawa.
Injiniya Muazu Magaji ya shiga cikin wadanda suka yafewa Dr. Abdullahi Umar Ganduje, amma ba zai manta abin da ya faru da Gwamnan ya bada umarni a kashe shi ba.
Wani matashi ne ya dankara ‘Dan majalisa da kasa bayan nasarorinsa a 2007, 2011, 2015 da 2019, hakan ya nuna Allah SWT ne yake bada mulki ga wanda ya so ga kowa
Gwamnonin jam’iyyar APC sun rubuta wasika domin ankarar da Bola Tinubu abin da ke faruwa. Akwai mutum biyu da ke kashe $500, 000 zuwa $1m domin samun mukami
Masu zafi
Samu kari