Shugaba Buhari Ya Sanya Baki a Rikicin Sudan, Ya Aike Da Wani Muhimman Sako

Shugaba Buhari Ya Sanya Baki a Rikicin Sudan, Ya Aike Da Wani Muhimman Sako

  • Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya nuna takaicin sa kan rikicin da ya ɓarke a ƙasar Sudan
  • Shugaba Buhari ya kuma yi kira ga ɓangarorin biyu masu faɗa da juna da tsagaita buɗe wuta su hau teburin sulhu
  • Rikcin neman karɓe ikon gwamnati ya ɓarke a Sudan a tsakanin ƴan tawaye da sojojin gwamnati

Makkah - Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yayi kira da a tsagaita buɗe wuta a ƙasar Sudan, biyo bayan rikicin da ya ɓarƙe a babban birnin ƙasar Khartoum, a tsakanin sojoji da ƴan tawaye.

Jaridar Punch tace shugaba Buhari ya bayyana cewa rikicin ba abin so bane, a yayin da shugaban miƙa mulki na ƙasar Chadi, Janar Mahamat Idriss Déby Itno, ya kai masa ziyara ranar Lahadi a birnin Makkah na ƙasar Saudiyya.

Kara karanta wannan

An Samu Asarar Rai Da Dukiyoyi Kan Mummunan Rikicin Sarauta a Wata Babbar Jihar Arewa

Shugaba Buhari ya yi kira a tsagaita wuta a Sudan
Fada ya barke a Khartoum babban birnin Sudan ranar Asabar 15 ga Afirilu 2023 Hoto: Von.com
Asali: UGC

A wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasa, Garba Shehu, ya fitar, shugaba Buhari ya kuma bayyana rikicin wanda ya lamushe rayukan ɗumbin mutane a matsayin abin takaici.

Shugabannin biyu sun yi duba kan lamarin inda suka yi kira ga dukkanin ƙasashen da ke maƙwabtaka da Sudan da kuma ƙasashen duniya da su sanya baki domin ganin ɓangarorin masu faɗa da juna sun zauna a teburin sulhu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaba Buhari ya yi nuni da cewa abin takaici ne halin da Sudan ta tsinci kanta a ciki, inda ya ƙara da cewa ƙasar ta cancanci samun zaman lafiya duba da halin da ta samu kanta a ciki a baya.

Shugaban ƙasar na Najeriya, ya kuma yabawa shugaban na Chadi bisa ƙoƙarin da yake na ganin abubuwa sun sassauta sannan su ci gaba da rayuwa cikin zaman lafiya, inda ya ce masa ya ci gaba da ƙoƙartawa.

Kara karanta wannan

Abu Ya Girma: Jam'iyyar APC Ta Dakatar da Ɗan Majalisar Tarayya Kan Babban Abu 1

Chadi ta nuna damuwar ta kan rikicin

Deby-Itno ya gayawa shugaba Buhari cewa halin da ake ciki a Sudan ya zama abin damuwa, cewar rahoton Arise News

"Abin takaicin shine idan ba a magance matsalar ba, rikicin zai samar da gagarumar illa ga ƙasashe masu maƙwabtaka da Sudan." A cewarsa.

A dangane da matakan da ƙasar sa ke ɗauka a dalilin ɓarkewar rikicin. Deby-Itno yace,

"Mun kulle iyakokin ƙasar mu da Sudan sannan mun ƙara ƙarfafa tsaron mu."

Mutane Da Dama Masu Azumin Jiran Haɗuwa Da Yesu Sun Kwanta Dama

A wani rahoton na daban kuma, kun ji yadda wasu masu azumin neman haɗuwa da Yesu suka kwanta dama.

Mutanen dai sun bazama cikin daji ne domin yin azumin bayan sun samu fatawa daga wani faston cocin da suke zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel