Mai Shekara 32 a Duniya Ya Doke ‘Dan Siyasar da Ya Shafe Shekara 16 Yana Majalisa

Mai Shekara 32 a Duniya Ya Doke ‘Dan Siyasar da Ya Shafe Shekara 16 Yana Majalisa

  • Bashir Usman Gorau aka sanar a matsayin wanda ya lashe zaben ‘dan majalisar Gada da Goronya
  • Hon. Musa S Adar ba zai koma Majalisar tarayya ba, bayan nasarorinsa a 2007, 2011, 2015 da 2019
  • Kafin nasarar zababben ‘dan Majalisar, yana cikin Kwamishinoni a Gwamnatin Aminu Tambuwal

Sokoto - Bashir Usman Gorau ya yi nasara a kan Musa S Adar a zaben majalisar wakilan tarayya da hukumar INEC ta karasa a karshen makon jiya.

Daily Trust ta kawo rahoto cewa Honarabul Musa S Adar ya rasa kujerarsa ta ‘dan majalisar mai wakiltar Gada da Goronya a hannun jam’iyyar PDP.

‘Dan takaran na PDP da ya doke Musa S Adar a zaben bana shi ne Kwamred Bashir Usman Gorau.

Kafin zamansa ‘dan takarar majalisa, Bashir Gorau mai shekara 33 da haihuwa shi ne tsohon Kwamishinan harkokin matasa da wasanni na Sokoto.

Kara karanta wannan

Matashi Ya Zama Zababben ‘Dan Majalisar Wakilai Yana ‘Dan Shekara 29 da Haihuwa

A karshe PDP ta karbe Gada/Goranyo

Rahoton ya ce Hukumar INEC ta tabbatar da Kwamred Gorau ya samu kuri’u 29, 679 a zaben, sai ‘dan majalisa mai-ci ya zo na biyu da kuri’u 25,549.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sakamakon zaben da aka kammala ya tabbatar da cewa zaman Honarabul Adar ya zo karshe a majalisa, bayan ya shafe shekaru 16 yana wakilci.

Mai Shekara 32 ya zama 'Dan Majalisa
Bashir Gorau zai zama 'Dan Majalisa Hoto: @bashirgorau
Asali: Facebook

Da a ce jam’iyyar APC ta yi nasara, za a rantsar da Adar a matsayin ‘dan majalisar Gada da Goronya a karo na biyar, ma’ana zai yi shekaru 20 a ofis.

The Cable ta ce tun bayan zaben 2007 ne Honarabul Adar ya tafi majalisa, a zabukan da aka shirya a 2011, 2015 da kuma 2019, duk shi ya samu nasara.

Mulki yana hannun Allah SWT

Da yake magana a shafinsa na Facebook a yammacin Lahadin da ta wuce, matashin ya godewa Allah SWT a kan wannan gagarumar nasara da ya samu.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC Ta Doke Manyan Abokan Karawarta, Ta Lashe Ƙarin Kujerun Yan Majalisa 8

Gorau ya jawo aya daga cikin Suratul Ali-Imran a Al-Kur’ani, yana nuna Ubangiji ne yake bada mulki ga wanda ya so, a lokacin da ya so, ga wanda ya so.

Wannan nasara ta na nufin an kara samun yawan matasan da za a rantsar a matsayin ‘yan majalisar tarayya, akwai sa’an Gorau da ya ci zabe a Kebbi.

"Gorau mutumin kirki ne"

Abubakar Umar Shattima wanda suka yi gwagwarmaya tare da zababben ‘dan majalisar a baya ya bayyana Bashir Gorau a matsayin jajirtaccen mutumi.

Shattima yake cewa ya san Gorau a matsayin mai kirki da taimakon matasa, musamman da ya rike kujerar Mai ba Gwamna shawara da Kwamishina.

A cewarsa, nasararsa a zaben darasi ce ga matasa, ya ce har abokan hamayyarsa su na murna.

Cin hanci a zaben Majalisa

Wasikar da Gwamnonin APC suka rubutawa Bola Tinubu ta nuna dole a dauki mataki a Majalisa, an ji labari ana jita-jita ana sayen kuri’un ‘yan majalisa.

Kara karanta wannan

Majalisar dattawa: APC ta lashe kujeru 59, an fadi yawan na PDP, NNPP, LP da SDP

Zargin da ake yi shi ne masu takara a majalisa sun shirya batar da $500, 000-$1m a kan kowace kuri’ar ‘dan majalisa da Sanata domin su lashe zabe mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel