Salon Hakimi: Matashi Ya Tada Kura a Intanet, Ya Sayi Kaya a Kasuwa, Ya Ce a Sanya Sunan Mahaifiyarsa a Rasiti

Salon Hakimi: Matashi Ya Tada Kura a Intanet, Ya Sayi Kaya a Kasuwa, Ya Ce a Sanya Sunan Mahaifiyarsa a Rasiti

  • Wani dan Najeriya ya jefa kafar sada zumunta a cece-kuce yayin da ya dabbaka labarin Achraf Hakimi da ake ta yada jita-jita akai
  • A madadin sunansa kan wasu takardunsa, matashin ya nemi a sanya sunan mahaifiyarsa kawai a jiki
  • Jama’ar kafar sada zumunta sun yi ca, sun bayyana ra’ayi da martaninsu game da wannan matashi

Najeriya - Wani dan Najeriya ya yanke shawarin bin salon Achraf Hakimi a lokacin da ya sayi wani abu, sai ya nemi a sanya sunan mahaifiyarsa a jikin rasitin.

Biyo bayan jita-jitan cewa, dan wasan kwallon kafa na PSG, Achraf Hakimi ya sanya sunan mahaifiyarsa kan dukkan kadarorinsa, ‘yan Najeriya, musamman maza sun so daukar salon.

A wani bidiyon da aka yada a TikTok, an ga lokacin da wani matashi ya sayi kayan N119k, sai yace a sanya sunan mahaifiyarsa a rasitin.

Kara karanta wannan

“Biza Dole”: Dattijuwar Mata Ta Shigo Najeriya Daga Amurka, Ta Yi Wuff Da Hadadden Saurayi a Bidiyo

Matashin da ya bi sahun Hakimi
Matashi ya sayi kaya ya saka sunan mahaifiyarsa | Hoto: @celebrity_amani
Asali: TikTok

A cewar matashin ga mai shago a lokacin da za a rubuta rasiti:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Sanya sunan uwata a can.”

Da yazo kafar sada zumunta yada bidiyon, sai ya rubuta shawari kamar haka:

“Ku ke sanya sunan mahaifiyarku kan komai.”

Kalli bidiyon:

Martanin jama’a

Agboola Anuoluwapo B:

"Na farko siyan katifa daga kamfanin Mouka, ka yi dabara. Na biyu amfani da sunan mahaifiyarka a kai wannan kuma zabi ne mai kyau.”

Iamsmall Baba:

"Daga sayen cajar waya kawai, kana son sanya sunan mahaifiyarka.”

Ayobami:

"Ta yaya ‘yan matan da ke tambayarmu 2k kullum za su ga 2k su karba tunda mu gayu sun waye dukkan kudadenmu sun koma asusun iyayenmu mata tun ranan Juma.a.”

Kofi AdMin:

"Mahaifiyata ta mutu amma zan sanya sunanta a haka.”

user5119510876694:

"Ina son koyon irin wannan yadda sunan mahaifiyata zan saka ko da a waya ta ne.:

Kara karanta wannan

Kano: Yan Sanda Sun Cafke Wasu Mutum 3 Bisa Tilasta Wani Almajiri Cin Bahaya Ana Azumi

Eric Richardstar:

"Sanya sunan ubana a can, kenan mahaifin ya mutu ko.”

Henry Jones:

"Ina fatan dai wannan yau faru ko.”

williamkelvin680:

"Dan uwa kada ka damu, komai yanzu sunan mahaifiyata na sanya.”

Budurwa ba za ta iya auren mai albashin N70k ba

A wani labarin kuma, kun ji yadda wata budurwa ta bugi kirji tace ba za ta iya auren wanda ke samun albashin N70,000 a wata ba.

Ta bayyana cewa, ita kanta kudin da take samu kenan, don haka ta san yawa da karancin kudin da take magana a kai.

Jama’ar kafar sada zumunta sun yi mamaki, sun bayyana yanayin da suka jii game da martanin wannan budurwar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel