Kwamishinan da Ganduje Ya Tsige Ya Yi Martani da Gwamna Ya Nemi Yafiyar Kanawa

Kwamishinan da Ganduje Ya Tsige Ya Yi Martani da Gwamna Ya Nemi Yafiyar Kanawa

  • Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya nemi afuwar ‘Yan jihar Kano, ya kuma yi wa kowa gafara
  • Muazu Magaji ya shiga cikin wadanda suka yafe, amma ba zai iya manta abin da ya faru ba
  • Injiniyan ya rike Kwamishinan ayyuka kafin Mai girma Gwamnan ya fatattake shi a 2020

Kano - Ganin wa’adinsa ya zo karshe, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya roki mutanen jihar Kano da su yafe masa duk wani laifi da ya yi masu.

An rahoto Mai girma Abdullahi Umar Ganduje yana cewa ya yi afuwa ga duk wani wanda ya yi masa wani laifi a tsawon shekarun da ya yi kan mulki.

Nan take sai aka ji tsohon Kwamishinan ayyuka da abubuwan more rayuwa na jihar Kano, Muazu Magaji ya yi martani zuwa ga Gwamna mai barin-gado.

Kara karanta wannan

Na Yafe Wa Kanawa Nima Ina Roko A Yafe Min, Gwamna Ganduje

Da yake magana a Facebook, Injiniya Muazu Magaji ya ce shi da iyalinsa sun yafewa Mai girma Gwamnana, amma akwai abin da za a su manta shi ba.

Zargin Gwamna da neman ganin baya

Magaji wanda aka fi sani da Dan Sarauniya yake cewa ba zai manta yunkurin tsohon mai gidansa, Gwamna Abdullahi Ganduje na ganin bayan shi ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

‘Dan siyasar da ya yi ta tsalle tsakanin wannan jam’iyya zuwa wannan a shekarar nan, ya jefi Dr. Ganduje da zargin neman hallaka shi a garin Abuja.

Tsohon kwamishinan ya kuma gagara mantawa da zaman gidan yarin da ya yi a kwanakin baya.

Ganduje
Gwamna Abdullahi Ganduje Hoto: @aabaji1
Asali: Facebook

“Ya Allah, a kan Sakon (Gwamna) Ganduje na neman yafiya. Ni da iyalina mun yafe masa.
Amma ba za mu manta da yunkurin hallaka mu da ya sa aka yi ba a Abuja, tare da Umra a kurmawa.”

Kara karanta wannan

Fintiri vs Binani: Gwamnan Adamawa ya yi bayani game da kitimurmurar zaben jihar

Da yake karin haske a shafinsa a karshen makon jiya, Dan Sarauniya ya ce afuwa ta na da kyau, amma ya ce a matsayinsa na ‘Dan Adam, ba zai manta ba.

Ragowar sakonnin Dansarauniya

Haka zalika jagoran na jam’iyyar APC mai ci ya ce ya kamata Gwamnan na Kano ya nemi yafiyar ragowar mutanen Arewa, domin mulkinsa ya shafe su.

“Ina ga fa yafiyar nan ba batun Kanawa kawai ake ba ..domin abubuwa da dama sun shafi mutuncin dukkan Yan Arewa.. musanman Musulmi!
Kuma ga sakon mutanen Dawakin Tofa...sunce a gayawa tsohon Gwamna..su ba a media su ka San shi ba... don haka ba sa cin mike...

“Allah SWT ne yake bada mulki”

A wani rahoton dabam, tsohon Kwamishinan Gwamna Aminu Tambuwal, Bashir Usman Gorau, ya kora wanda ya yi shekaru 16 a Majalisa zuwa gida.

Kafin PDP ta kawo karshensa a bana, ‘Dan majalisar na Goranyo da Gada, Hon. Musa S. Adar ya lashe zabukan majalisar tarayya na 2007, 2011, 2015 da 2019.

Kara karanta wannan

Zababben ‘Dan Majalisar Kano a Jam’iyyar NNPP Ya Rasa Kujerarsa a Gwamnatin Buhari

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng