NDLEA Ta Kama Mata Mai Juna Biyu Da Wani Gurgu Kan Safarar Miyagun Kwayoyi A Edo

NDLEA Ta Kama Mata Mai Juna Biyu Da Wani Gurgu Kan Safarar Miyagun Kwayoyi A Edo

  • Jami'an hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi (NDLEA) sun yi ram da wata mata mai juna biyu dillaliyar miyagun ƙwayoyi
  • Jami'an sun kuma cafke wani gurgu mai irin wannan baƙar sana'ar a jihar Edo da ke Kudancin Najeriya
  • Jami'an na NDLEA sun kuma yi caraf da wani matafiyi ɗauke da miyagun ƙwayoyi yana shirin barin Najeriya

Jihar Edo - Jami'an hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA) a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Legas, sun cafke wata mata mai juna biyu mai suna, Rabetu Abdulrasak, mai shekara 24 a duniya da miyagun ƙwayoyi a jihar Edo.

Jami'an sun cafke matar mai suna biyu ne tare da wani gurgu mai suna Shehu Adams, a Agbede, cikin ƙaramar hukumar Etsako ta Yamma a jihar Edo, a ranar Asabar 15 ga watan Afirilun 2023, rahoton Vanguard ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Shin An Biya Kuɗin Fansa? Ɗalibai Mata Na Jami'ar Tarayya Gusau Sun Kubuta Daga Hannun Yan Bindiga

Jami'an NDLEA sun cafke wata mata mai juna biyu da gurgu masu safarar miyagun kwayoyi
Mata mai juna biyu da gurgu masu safarar miyagun kwayoyi da jami'an NDLEA suka cafke a Edo Hoto: PRNigeria.com
Asali: UGC

An kuma samu miyagun ƙwayoyi da suka haɗa da tabar wiwi, methamphetamine, tramadol da swinol.

Kakakin hukumar Femi Babafemi shine ya tabbatar da cafke mutanen biyu a wata sanarwa da ya fitar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A kalamansa:

"Jmi'an NDLEA sun cafke wata matar aure mai suna Rabetu Abdulrasak, mai shekara 24 da wani gurgu Shehu Adams, a Agbede, cikin ƙaramar hukumar Etsako ta Yamma, inda suka kwato sama da kilogiram 14 na miyagun ƙwayoyi ,
Wadanda suka haɗa da tabar wiwi, methamphetamine, tramol da swinol, a ranar 15 ga watan Afirilu."

PR Nigeria tace hukumar ta kuma cafke tulin wasu miyagun ƙwayoyi da suka haɗa da Tramol, Rohypnol, Ecstasy da tabar wiwi da aka ɓoye a cikin rigunan sanyi da ƙwalaben man shafawa.

An cafke tulin miyagun ƙwayoyin ne a filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke a Legas a ranar 14 ga watan Afirilun 2023, bayan an kama wani fasinja mai suna Joshia Sunday, wanda zai yi tafiya kan jirgin saman Qatar ta hanyar Doha zuwa Oman.

Kara karanta wannan

Abu Ya Girma: Jam'iyyar APC Ta Dakatar da Ɗan Majalisar Tarayya Kan Babban Abu 1

Femi Babafemi, ya ce bayan an yi wa jakunkunan wanda ake zargin binciken ƙwaƙwaf, an samu 4.80kg na tabar wiwi wacce aka ɓoye a cikin rigunan sanyi uku da kuma adadi daban-daban na Tramol, Rohypnol, Ecstasy da aka ɓoye a cikin ƙwalaben man shafawa.

Jami'an NDLEA Sun Cafke Wata Tsohuwa Mai Safarar Miyagun Kwayoyi

A wani labarin na daban kuma, wata tsohuwa mai safarar miyagun kwayoyi ta faɗa komar jami'an hukumar NDLEA a jihar Rivers.

Jami'an hukumar sun samu nasarar ƙwace miyagun ƙwayoyi a hannun tsohuwar waɗanda kuɗin su ya kai miliyoyin naira.

Asali: Legit.ng

Online view pixel