Latest
An shiga zullumi bayan ƴan bindiga sun yi awon gaba da sakataren tsare-tsaren j'iyyar All Progressives Congress (APC) na jihar Kaduna bayan sun farmake shi.
Gwamnan jihar Imo, Mr Hope Uzodinma, ya faɗa wa ma'aikatan jihar da suka ziyarce shi cewa ya cika alƙawurran da ya ɗaukar musu baki ɗaya har da karin wasu.
Shugabannin jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) na jihohi, ba su gamsu da hukuncin ƴan kwamitin NWC suka ɗauka ba na dakatar da Dr Boniface Aniebonam.
Hukumar 'yan sanda reshen jihar Benuwai ta sanar da cewa dakarunta sun yi nasarar kama mutum ɗaya da ake zargin yana da hannu a kisan mai shari'a mai ritaya.
Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya koka kan kudaden tallafi na Shugaba Tinubu, ya ce Naira biliyan biyu ne kawai su ka shigo asusun gwamnatinsa.
Shahararren jarumin nan da masana'antar shirya fina-finan Hausa, Ali Nuhu, wanda aka fi sani da Sarkin Kannywood, ya bayyana dalilin da yasa ya ki kara aure.
Gwamnatin sojin jamhuriyar Nijar ta kori jakadan Faransa, Sylvain Itte, bisa ƙin amsa gayyatar da ta aiko masa, ta gindaya masa wa'adin awanni 48 ya bar ƙasar.
Jihar Kaduna ba ta da wakili har yanzu a cikin ministocin Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu. Wata ƙungiya daga Kudancin Kaduna ta buƙaci a ba yankin kujerar.
Wata jami'ar yan sanda, Insufekta Charity ta sha yabo da kyautar N250,000 daga kwamishinan yan sandan jihar Anambra kan ta ƙi karban cin hanci daga wani mutumi.
Masu zafi
Samu kari