“Budurwarsa Ta Ba Shi Kunya”: Malamin Addini Ya Yi Tsalle Daga Ginin Bene Mai Hawa 2, Ya Mutu a Anambra

“Budurwarsa Ta Ba Shi Kunya”: Malamin Addini Ya Yi Tsalle Daga Ginin Bene Mai Hawa 2, Ya Mutu a Anambra

  • Wani fasto mai shekaru 30, Prosper Igboke, ya yi mutuwar bakin ciki ta hanyar fadowa daga ginin bene mai hawa biyu a yankin Nnewi, jihar Anambra
  • An yi zargin cewa faston ya dauki matakin dira daga benen saboda budurwarsa da ya dauki nauyin karatunta har jami'a ta bada masa kasa a ido
  • Yan uwan Igboke sun bayyana cewa saboda kashe kansa da ya yi, za a binne shi ne a cikin jeji kamar yadda yake bisa al'ada

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Nnewi, jihar Anambra - Rahotanni sun kawo cewa Fasto Prosper Igboke, mai shekaru 30 ya yi tsalle ya duro daga ginin bene mai hawa biyu a Nnewi, jihar Anambra.

Marigayin, wanda ya kasance fasto a cocin Pentecostal, ya yi tsalle daga ginin benen sakamakon kasa da budurwarsa ta bada masa a ido, jaridar The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

Kannywood: Ali Nuhu Ya Bayyana Dalilin Da Yasa Bai Kara Aure Ba

Fasto ya kashe kansa a kan budurwa
An yi amfani da horon don misali ne kawai. Wadanda ke hoton ba su da alaka da batun da ake magana kansa a rahoton
Asali: Getty Images

Wani dan uwan marigayin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce budurwar ta ki amsa tayin aurensa bayan ya gama daukar dawainiyarta har ta gama jami'a.

"Lamarin ya faru ne a watan jiya. Ya kasance dan shekara 30 a lokacin da ya mutu. Budurwarsa, wacce ya yi niyar aura ta ba shi kunya bayan ya gama daukar dawainiyarta har zuwa jami'a.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ya yi tsalle daga ginin bene mai hawa biyu sannan ya mutu. Na yi mamaki cewa mutuwan wannan shekaru kuma fasto zai iya yin wannan," inji dan uwan nasa.

Za a binne Prosper Igboke a dokan daji

A cewar dan uwan nasa, za a binne Igboke wanda ya kasance dan Umunneochi, jihar Abia a dokan daji saboda ya kashe kansa.

Ya ce:

"Za a binne shi a daji saboda kashe kansa kamar yadda yake bisa al'adar al'ummar Leru na karamar hukumar Umunneochi a jihar Abia.

Kara karanta wannan

"Kyau Iya Kyau": Bidiyon Jarumar Fim Da Biloniyan Mijinta a Wajen Bikin Diyar Sanata Sani Ya Girgiza Intanet

A cewar jaridar Nigerian Tribune, daga karshe an binne marigayin a wani daji da ke garinsu.

Amarya ta fadi ta mutu a ranar aurenta

A wani labari na daban, mun ji cewa wata amarya mai suna Rebecca Oyedotun, ta yanke ciki ta fadi matacciya a ranar aurenta a yankin Ogbomoso da ke jihar Oyo.

Mummunan al'amarin ya afku ne a jajiberin ranar aurenta yayin da ake bikin wankar amarya tare da kawayenta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel