Shugaban Gwamnonin Arewa, Inuwa Yahaya Ya Koka Kan Tallafin Tinubu, Ya Shawarci Mutane Su Rungumi Harkar Noma

Shugaban Gwamnonin Arewa, Inuwa Yahaya Ya Koka Kan Tallafin Tinubu, Ya Shawarci Mutane Su Rungumi Harkar Noma

  • Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya koka kan kudaden tallafin Gwamnatin Tarayya
  • Inuwa ya ce ba kamar yadda mutane ke tunani ba, Naira biliyan biyu ne kawai ya shigo musu
  • Legit.ng Hausa ta ji ta bakin wasu mazauna garin Gombe inda su ka bayyana ra'ayoyinsu kan kudaden

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Gombe - Gwamnan jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya ya ce Naira biliyan biyu kawai ya samu daga biliyan biyar na Gwamnatin Tarayya game da kudaden rage radadin cire tallafi.

Yahaya wanda shi ne shugaban gwamnonin Arewacin Najeriya ya bayyana haka yayin rarraba kayan agaji na karshe ga mutane a fadar Sarkin Gombe a ranar Laraba 23 ga watan Agusta.

Gwamna Inuwa na Gombe ya yi martani kan kudaden tallafin Shugaba Tinubu
Shugaban Gwamnonin Arewa, Inuwa Yahaya Ya Yi Martani Kan Tallafin Tinubu. Hoto: Isma'ila Uba Misilli.
Asali: Twitter

Meye Inuwa ya ce game da tallafin Tinubu?

Daga cikin kayan da aka rarraban akwai shinkafa da takin zamani da taliya da kuma maganin kwari da sauransu.

Kara karanta wannan

Ikon Allah: Gwamnan Arewa Ya Lale Kudi Sama da Biliyan Ɗaya Ya Siyo Motoci 10 Domin Taimaka Wa Talakawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya ce ba kamar yadda mutane ke tunani ba, Naira biliyan biyu ce kawai ta shigo asusun jihar daga Gwamnatin Tarayya inda ya ce babu abin da za su yi sai dai rage yunwa.

Legit.ng Hausa ta tattauna da wasu mazauna birnin Gombe kan kudaden tallafin inda su ka bayyana ra'ayoyinsu mabambanta.

Meye mutane ke cewa game da tallafin Tinubu?

Honarabul Abubakar Auwal Akko, jigo a jam'iyyar APC ya ce daman tun kafin wannan lokaci tuni gwamna Inuwa ya ke rabon kayan tallafi ga talakawan jihar.

Ya ce akalla gwamnatin ta raba wa mutane taki da abinci fiye da 420,000 a fadin jihar.

Ya kara da cewa a tunaninsa Gwamnatin Tarayya ma kwaikwayon gwamnan jihar ta yi inda ya ce bisa ga tsarin da aka bi, babu inda tallafin ba zai zaga ba.

Kara karanta wannan

Cire Tallafi: Tinubu Ya Nemo Hanyar Sauki, Zai Samar Da Sabbin Gidajen Mai 9,000 Madadin Na Fetur, Bayanai Sun Fito

Architect Akko ya ce gwamnan da wasu na kusa da shi musamman Usman Bello Kumo mai wakiltar mazabar Akko a majalisar wakilai sun raba kayan agaji ganin irin halin da ake ciki.

Ana shi martanin, Khalid Ibrahim ya ce daman sun san gwamnan ba raba kayan zai yi ba, kuma ba sa bukatar ya shawarce su, su kama harkar noma daman da ita ya gansu.

Honarabul Aishatu Chiroma ta ce matsalar da ake samu 'yan handama ake bai wa kayan su raba wanda hakan ba ya isa inda ya kamata.

Ta ce a lokacin siyasa an yi ta rabawa mutane rubabben abinci tun na lokacin 'Korona' inda ta ce akwai abinci a cike a rumbun gwamnati amma ba za a taimaki mutane ba duba da irin halin da su ke ciki ba.

Yayin da Aisha Muhammad ta ce idan har za a raba yadda ya kamata to gaskiya hakan zai taimaka.

Kara karanta wannan

Cire Tallafi: Kwastomomi Sun Rage Zuwa Gida Karuwai a Kano, Gidan Magajiya Ya Dauki Zafi

Sai dai ta ce mafi yawanci irin wannan tallafi ba ya isa inda ya kamata sai dai ka ji ana yi idan baka san kowa ba.

Inuwa Yahaya Ya Zama Sabon Shugaban Gwamnonin Arewa

A wani labarin, Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya zama sabon shugaban gwamnonin Arewa.

Inuwa ya gaji tsohon gwamnan jihar Plateau, Simon Bako Lalong a matsayin sabon shugaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel