Jarumin Kannywood Ali Nuhu Ya Bayyana Dalilin Da Yasa Bai Kara Aure Ba

Jarumin Kannywood Ali Nuhu Ya Bayyana Dalilin Da Yasa Bai Kara Aure Ba

  • Sarkin Kannywood, Ali Nuhu ya magantu a kan dalilinsa na kin yi wa matarsa, Maimuna kishiya tsawon shekaru
  • Jarumin da matarsa sun shafe tsawon shekaru 20 tare kuma suna da 'ya'ya biyu a tsakaninsu
  • Ali ya bayyana cewa sam auren mace fiye da daya baya cikin tsarinsa kuma yana ganin hakan ya fi masu zaman lafiya da kwanciyar hankali

Fitaccen jarumin Kannywood, Ali Nuhu, wanda aka fi sani da Sarkin Kannywood, ya bayyana dalilin da yasa yake zaune da mace daya tsawon shekaru da sama da ashirin.

Ali Nuhu ya ce auren mata fiye da daya baya burge shi
Jarumin Kannywood Ali Nuhu Ya Bayyana Dalilin Da Yasa Bai Kara Aure Ba Hoto: Ali Nuhu Mohammed
Asali: Facebook

Idan kana zaman lafiya da matarka baka bukatar kara aure, Ali Nuhu

Da ake zantawa da shi a shirin Gabon Show Room na jaruma Hadiza Gabon, Ali ya bayyana cewa duk da kasancewarsa Musulmi, sam ra'ayin tara mata baya cikin tsarinsa sam baya burge shi.

Kara karanta wannan

Kano: Kotun Shari’a Ta Bai Wa Magidanci Masauki a Gidan Yari Kan Lakadawa Tsohuwar Matarsa Duka

Ya ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Na yi aure kusan shekaru ashirin kenan kuma kwanaki muka yi murnar cika shekarunmu 20 da aure tare da matata. Na yi aure a 2003 kuma yanzu muna 2023.
"Ni yadda nake kallon lamarin aure na kalle shi kamar wanda idan kai da matarka kuna da fahimta, sa'annan da kuma soyayya har ka lura cewa shigowar wata ba zai sa ka iya yin adalci ba na farko, ko kuma shigowar wata zai iya dan kawo tangarda da rauni ga yanayin zamantakewarku toh ina ganin gwanda kawai ka zauna da matarka.
"Musamman ma idan ka yi la'akari da cewa shi dai aure ana yin shi ne don a samu zuri'a kuma Alhamdulillahi mun samu, muna da yarmu Fatimah, muna da danmu Ahmad, don haka ina ganin babu abin da ya fi kwanciyar hankalinmu da zaman lafiyarmu a yanzu."

Kara karanta wannan

Shigar Nuna Tsaraici Da Matar Fitaccen Mawakin Amurka Tayi Ya Fusata Mutanen Italiya, Sun Nemi a Kore Ta

Kan ko sune suka kayyade yara biyu za su haifa a duniya, jarumin ya ce:

"Haka Allah ya nufa, ni a zabina na so na yi yara hudu ne."

Amal Umar ta bayyana abun da ke tsakaninta da tsohon saurayinta

A wani labarin kuma, fitacciyar jarumar Kannywood, Amal Umar, ta bayyana ainahin abun da ya faru kan zargin da wani tsohon saurayinta ke mata na cinye masa kudi.

Amal dai tana fuskantar tuhuma daga wani tsohon saurayinta kan damfarar kudi wanda yawansu ya kai kimanin Naira miliyan 40.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel