Ministan Makamashi Ya Bayyana Lokacin Da Za a Samu Wadatacciyar Wutar Lantarki a Najeriya

Ministan Makamashi Ya Bayyana Lokacin Da Za a Samu Wadatacciyar Wutar Lantarki a Najeriya

  • Ministan makamashi na Najeriya ya bayar da tabbacin matsalar rashin wadatacciyar wutar lantarki ta kusa zuwa ƙarshe
  • Adebayo Adelabu ya bayyana cewa nan da wata shida zuwa shekara ɗaya lantarkin da ake samu a ƙasar nan za ta ƙaru
  • Ministan ya yi nuni da cewa akwai jan aiki kafin tabbatuwar hakan amma abu ne wanda za a iya cimmawa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Oyo - Ministan makamashi, Adebayo Adelabu, ya bayyana cewa ƴan Najeriya za su fara ganin sauyi wajen samun wadatacciyar lantarki a ƙasar nan.

Adebayo Adelabu ya bayyana cewa nan da wata shida zuwa shekara ɗaya ƴan Najeriya za su riƙa samun wadatacciyar wutar lantarki, cewar rahoton The Cable.

Adelabu ya bayyana lokacin da za a samu wutar lantarki Najeriya
Adelabu ya ce nan da wata shida zuwa shekara daya wutar lantarki za ta wadata Hoto: Bayo Adelabu
Asali: Facebook

Ministan makamashin yana daya ɗaga cikin ministocin da Shugaba Bola Tinubu ya rantsar a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Akpabio Ya Ce Ya Kamata Maza Su Duba Yiwuwar Mika Ragamar Siyasa Ga Mata Su Koma Gefe, Ya Bada Dalili

Akwai jan aiki wajen samar da wutar lantarki, Adelabu

Da yake tattaunawa da manema labarai a filin tashi da saukar jiragen sama na Ladoke Akintola a birnin Ibadan, babban birnin jihar Oyo, Adelabu ya bayyana cewa akwai jan aiki a gaba amma za a iya yin nasara.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya bayyana cewa aikin samar da wadatacciyar wutar lantarkin ba abu ba ne wanda za a iya cimmawa cikin ƙanƙanin lokaci, amma za a cimmasa idan aka yi abin da ya dace.

A kalamansa:

"Ina faɗa muku cewa tsakanin wata shida zuwa shekara ɗaya, za mu fara ganin cigaba a ɓangaren wutar lantarki"
"Nan da wata shida masu zuwa, za a samu ƙarin wutar lantarki a layin raba wuta na ƙasa, aikin samar da ƙarin wutar lantarki 700mw na Zungeru a jihar Neja ya kusa kammaluwa."

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Wata Kungiya Ta Bukaci Ministocin Tinubu Su Yi Murabus, Ta Bayyana Dalilanta

"Wannan shi ne zai zama wanda babu kamarsa a yankin Saharar Afirika idan aka kammala aikinsa."
"Wannan sabon lokaci ne, sannan zan yi amfani da dukkanin abin da Allah ya ba ni domin tabbatar da cewa muna da wadatacciyar wutar lantarki a ƙasar nan."

Hannatu Musawa Ba Ta Kammala NYSC Ba

A wani labarin kuma, hukumar ƴan yiwa ƙasa hidima (NYSC) ta tabbatar da cewa ministar fasaha, al'adu da tattalin arziƙin fikira, Hannatu Musa Musawa, ba ta kammala bautar ƙasa ba.

Hukumar ta yi bayanin cewa a yanzu ministar ke yin bautar ƙasarta, sannan ta sha alwashin ɗaukar matakin da ya dace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng