Dan Najeriya Ya Daka Tsalle Ya Fada Kogin Legas, ’Yan Sanda Sun Magantu

Dan Najeriya Ya Daka Tsalle Ya Fada Kogin Legas, ’Yan Sanda Sun Magantu

  • Rundunar 'yan sanda ta fara bincike kan yadda wani mutumi da ya nutse a cikin tekun Legas a kokarin tserewa wani mai shagon siminti
  • Kakakin rundunar na jihar Legas, Benjamin Hundeyin ya ce matashin ya fada kogin ne bayan an zarge shi da satar buhunan siminti
  • Daraktan hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Legas (LASEMA) shiyyar Legas ta tsakiya ne ya kai rahoton lamarin ga 'yan sandan Ikoyi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Legas - Rahotanni sun bayyana cewa wani mutum da aka bayyana sunansa da Azeez ya ya daka tsalle ya fada kogin Legas.

Ana zargin mutumin ya fadi kogin ne ta bangaren gadar Lekki-Ikoyi da safiyar Juma’a bayan an zarge shi da satar wasu buhunan siminti.

Kara karanta wannan

"Shi ke haukata 'yan kasa", Malamin addini a Kaduna ya ja kunnen Tinubu kan halin kunci

Dan Najeriya ya nutse a tekun Legas kan zargin satar siminti
'Yan sanda na bincike a kan mutumin da ya fada tekun Legas. Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Benjamin Hundeyin, mai magana da yawun ‘yan sanda a Legas, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Lahadi, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hundeyin ya ce daraktan da ke kula da ayyukan hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Legas (LASEMA) shiyyar Legas ta tsakiya ne ya kai rahoton lamarin a Ikoyi.

Ana zargin Azeez ya saci buhunan siminti

Hundeyin ya ce a lokacin da jami’an ceto suka isa wurin, sun tarar da gawar wani mutum da ya halaka a cikin ruwan bayan ya nutse.

“Bayan bincike, an gano cewa sunan marigayin a Azeez. Daga baya ne ma’aikatan lafiya na Pre Hospital Care, Legas suka tabbatar da rasuwarsa.”
"An gano cewa wani mai sayar da siminti mai suna Iliya Amos ke bin bayan mamacin kafin ya fada cikin tekun saboda yana zarginsa da sace wasu buhunan siminti."

Kara karanta wannan

Shirin ba ɗalibai rancen kuɗi; Tinubu ya naɗa Jim Ovia a matsayin shugaban NELFund

- A cewar Hundeyin.

Jaridar Tribune ta rahoto kakakin ya ce ‘yan sanda za su gano gaskiya a kan lamarin, inda ya kara da cewa an dauki gawar zuwa dakin ajiyar gawarwaki domin gudanar da binciken gawa.

Sojoji sun dakile harin Taraba

A wani labarin kuma, rundunar sojoji ta ce dakarunta da ke atisayen 'Whirl stroke' a sun dakile wani hari da 'yan bindiga suka kai kauyen Kweserti da ke Ussa a jihar Taraba.

Bayan artabu da 'yan bindigar, sojoji sun yi nasasar kashe 'yan ta'adda biyu tare da kwato makamai da suka hada da bindiga da alburusai masu yawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel