“Abin da Ya Zama Dole Ne”: Gaskiyar Dalilin da Ya Sa Tinubu Ya Janye Tallafin Man Fetur

“Abin da Ya Zama Dole Ne”: Gaskiyar Dalilin da Ya Sa Tinubu Ya Janye Tallafin Man Fetur

  • Shugaban kasa Bola Tinubu ya ce daina biyan tallafin man fetur da gwamnatinsa ta yi ya zama wajibi domin daidaita tattalin arzikin kasar
  • A cewar shugaban kasar, idan da bai janye tallafin ba, to da yanzu Najeriya ta fada cikin fatara wanda ba lallai ta iya fita a karamin lokaci ba
  • Tinubu ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a taron tattalin arzikin duniya da ke gudana a birnin Riyadh na kasar Saudiyya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Riyadh, Saudiyya - Shugaba Bola Tinubu ya dage kan cewa matakin da gwamnatinsa ta dauka na cire tallafin man fetur ya zama wajibi domin hana kasar fadawa cikin fatara.

Kara karanta wannan

Ana murna sauƙi ya fara samuwa, Tinubu ya sake tsoratar da 'yan Najeriya, ya yi jan ido

Tinubu ya yi magana kan janye tallafin man fetur a Saudiya
Tinubu ya kare gwamnatinsa kan matakain daina biyan tallafin man fetur. Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Tinubu ya sanar da daina biyan tallafin man fetur ne a ranar da aka rantsar da shi tare da furta kalmar “biyan tallafi ya kare”.

Janye tallafin fetur ya jawo cece-kuce

Sai dai matakin ya sa farashin kayayyaki ya tashi sama, lamarin da ya kara wahalhalu a kasar tare - rufe iyakokin kasar ya kara ta'azzara lamarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Halin kunci da kasar ta tsinci kanta ya sanya wasu daga cikin masu sukar gwamnatinsa suka yi Allah wadai da janye tallafin, suna masu cewa babu hangen nesa a daukar matakin.

Amma Tinubu ya bayar da hujjar cire tallafin man fetur, yana mai cewa ana bukatar a sake farfado da tattalin arzikin kasar ne farko a kan komai, rahoton Channels TV.

Tinubu ya fadi dalilin janye tallafin fetur

Kara karanta wannan

"Shi ke haukata 'yan kasa", Malamin addini a Kaduna ya ja kunnen Tinubu kan halin kunci

Tinubu ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a matsayin daya daga cikin mahalarta taron tattalin arzikin duniya da ke gudana a birnin Riyadh na kasar Saudiyya a safiyar yau.

"Ga Najeriya, mun yi imanin cewa haɗin gwiwar tattalin arziki da haɗa kai ya zama dole domin samar da daidaito a lamuran sauran kasashen duniya.
"Game da batun cire tallafin fetur, ko shakka babu ya zama wajibi domin kare kasata daga fadawa talauci, da kuma sake saita tattalin arziki da hanyar ci gaban kasar."

- A cewar Tinubu.

Tinubu ya amince ana wahala a Najeriya

A cewar rahoton Arise News, Tinubu ya amince da matsalar da ke tattare da matakin da ya dauka na yin watsi da biyan tallafin wanda ya bai wa ‘yan Najeriya damar sayen mai a farashi mai rahusa.

Tinubu ya kara da cewa.

"Na san cewa wannan mataki ne mai wahalar gaske, amma alamar shugabanci na-gari shine yanke hukunci mai tsauri a lokacin da ya kamata a yanke irin hukuncin."

Kara karanta wannan

Kamfanin NNPC ya shawo kan matsalar da ta kawo dogon layi a gidajen mai

Tinubu ya ba Jim Ovia mukami

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa, shugaban kasa Bola Tinubu ya nada Mr. Jim Ovia a matsayin shugaban hukumar ba da lamunin karatu ta Najeriya (NELFund).

Ovia wanda shi ne ya kafa bankin Zenith, zai jagoranci NELFund da manufar tallafawa dalibai da matasan Najeriya wajen yin ilimi mai zurfi da bunkasa sana'o'in su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel