"Yadda Murtala Mohammed Ya Mutu Bai Bar Komai Ba a Rayuwarsa", Tsohon Minista Ya Magantu

"Yadda Murtala Mohammed Ya Mutu Bai Bar Komai Ba a Rayuwarsa", Tsohon Minista Ya Magantu

  • An bayyana tsohon shugaban kasa a mulkin soja, Janar Murtala Mohammed a matsayin mutum mai kan-kan da kai a rayuwa
  • Ambasada Aminu Bashir Wali ya ce Murtala bai saci ko kwabon Najeriya ba inda ya tabbatar da cewa Janar din ya mutu bai bar komai ba
  • Tsohon jakadan kasar Sin, Wali ya bayyana haka ne a yau Lahadi 28 ga watan Afrilu yayin hira da 'yan jaridu a jihar Kano

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Tsohon ministan harkokin waje, Ambasada Aminu Bashir Wali ya yi magana kan rayuwar tsohon shugaban kasa, Janar Murtala Mohammed.

Ambasadan ya ce tsohon shugaban mukin soja ya bar duniya bai mallaki komai ba a rayuwarsa.

Kara karanta wannan

Yahaya Bello: Tsohon shugaban APC ya dauki zafi kan dambarwar, ya soki gwamna mai ci

Yadda tsohon shugaban kasa, Murtala Mohammed ya bar duniya ba ko sisi
Bashir Wali ya bayyana Janar Murtala Mohammed wanda bai damu da abin duniya ba. Tarihi TV.
Asali: Facebook

Yadda halayen Murtala Mohammed su ke

Wali ya bayyana haka ne yayin hira da jaridar Daily Trust a yau Lahadi 28 ga watan Afrilu a jihar Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana Janar Murtala a matsayin mutum mai saukin kai da tsoron abin duniya wanda bai taba daukar kwabon gwamnati ba.

"Daga cikin dukkan 'yan uwanmu, nine mafi kusa da Murtala, na fi kusa da shi a kan sauran 'yan uwana."

- Bashir Wali

Wali ya ce Murtala bai bar komai ba

Da aka tambaye shi kan zargin mutane na cewa tsohon shugaban ya kwashe kudin al'umma, Wali ya ce:

"Ban san wannan ba, Murtala ya na taka tsan-tsan da sha'anin kudi, wannan ba layinsa ba ne."
"Murtala ya kare martabarsa, ina mai tabbatar maka da cewa ya mutu bai bar komai ba a duniya."

Kara karanta wannan

Ana murna sauƙi ya fara samuwa, Tinubu ya sake tsoratar da 'yan Najeriya, ya yi jan ido

Ambasadan ya ce Murtala ya kan dawo gida tun kafin zama shugaban ƙasa ya ce ba shi da kudin biyan kudin makarantar yara.

Ya ce kwata-kwata ba ya jin kunyan hakan, kuma zai iya fadamin ko wani daga cikin abokansa ba tare da jin komai ba.

EFCC na tuhumar Yahaya Bello kan badakalar N84bn

A wani labarin, Hukumar EFCC ta na tuhumar tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello kan badakalar N84bn.

Hukumar ta na tuhumar tsohon gwamnan ne da badakalar kudin lokacin da ya ke mulkin jihar kafin mika mulki ga Gwamna Usman Ododo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel