Latest
A zaman da ta yi na yau Talata, 30 ga watan Afrilu, majalisar wakilai ta bukaci hukumar NERC da ta dakatar da aiwatar da sabon kudin wutar da ta sanar a baya.
Jam'iyyar PDP a matakin gundumar ta dakatar da Awaji-Inombek Abiante, dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Andoni/Opobo a jihar Ribas a ranar Litinin.
Dalibar jami'ar Abuja da ta bata ranar Jumu'ah ta rasu a hatsarin mota a hanyar Ludbe. Iyalan dalibar ne suka fitar da sanarwa a jiya Litinin da yamma
Mai Shari'a, Farouk Adamu, shugaban kwamitin binciken shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Ganduje ya ce za su yi duba na musamman kan zargin badakalar da aka tafka.
Kasa da mako daya da 'yan bindiga suka kai hari yankin Dutse da ke Bwari, babban birnin tarayya Abuja, 'yan bindigar sun sake kai wani sabon harin a daren Talata.
Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da kafa dokar gwajin lafiya kafin aure a fadin jihar. A jiya Litinin ne majalisar ta gama karanta kudurin dokar
Hukumar shirya jarrabawa ta JAMB ta bayyana cewa kaso 76% daga cikin dalibai kusan miliyan biyu da suka rubuta jarrabawar UTME sun gaza cin maki 200.
Bayan fama da rashin ruwan sha a jihar Gombe, gwamnatin jihar ta yi alkawarin magance matsalar zuwa ranar Laraba. Gwamnan jihar ne ya bayyana haka a jiya Talata
Yayin da ake tunkarar zaben 2027, akwai alamu wasu jiga-jigan APC za su iya bijirewa Shugaba Bola Tinubu a zaben saboda wasu matsaloli da ke faruwa.
Masu zafi
Samu kari