'Yan Bindiga Sun Shiga Garuruwa, Sun Hallaka Mutum 10, Ɗan Majalisa Ya Magantu

'Yan Bindiga Sun Shiga Garuruwa, Sun Hallaka Mutum 10, Ɗan Majalisa Ya Magantu

  • An shiga tashin hankali bayan 'yan bindiga sun kai mummunan hari a kananan hukumomi biyu da ke jihar Binuwai
  • Maharan sun kai harin ne kananan hukumomin Agatu da Gwer ta Gabas inda suka yi ajalin akalla mutane 10 yayin harin
  • Sai dai kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, SP Catherine Anene ta ce ba ta da masaniya kan sabon harin da ya faru

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Benue - Rahotanni sun nuna cewa an kashe mutane 10 a wasu hare-hare daban-daban da aka kai a kananan hukumomin Agatu da Gwer ta Gabas a jihar Binuwai.

Yayin da ‘yan bindiga suka kashe mutane biyar a kauyukan karamar hukumar Agatu, an kuma kashe wasu biyar a gundumar Mbasombo da ke karamar hukumar Gwer ta Gabas.

Kara karanta wannan

An kama mutum 2 yayin da wani gini mai bene ya kashe mutane a jihar Kano

'Yan bindiga sun kai wani sabon hari tare da hallaka mutane 10
'Yan bindiga sun yi ajalin mutane 10 a ƙananan hukumomi 2 a Binuwai. Hoto: Nigeria Police Force.
Asali: Twitter

Yaushe 'yan bindiga suka kai harin?

Mazauna yankin sun ce an kai hare-haren ne a ranar Lahadin da ta gabata a wasu kauyuka uku na Agatu, yankin kamun kifi mai iyaka da jihar Nasarawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani mazaunin yankin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyanawa Daily Trust cewa:

"A jiya Lahadi 28 ga Afrilun 2024, makiyaya dauke da makamai sun kashe mutane biyar a karamar hukumar Agatu."

'Dan majalisa ya koka kan harin

Wani mamba mai wakiltar mazabar Agatu a majalisar dokokin jihar, Godwin Abu Edoh, ya tabbatar da kashe-kashen, inda ya koka da cewa lamarin ya zama ruwan dare, cewar Tori News.

Da aka tuntubi jami’ar hulda da jama’a ta rundunar ‘yan sanda (PPRO), SP Catherine Anene, ta ce ba ta da masaniya kan sabon lamarin da ya faru a Agatu.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kai sabon hari mahaifar ministan Tinubu, sun tafka babbar barna

Gwamnan Binuwai ya gargadi tsoffin gwamnoni

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Hyacinth Alia na jihar Binuwai ya gargadi tsoffin gwamnonin jihar kan tsoma baki a harkokin mulkinsa.

Alia ya ce idan har ba za su taimakawa jihar wurin samun ci gaba to su yi shiru da bakinsu su bar shi ya ci gaba da ayyukan alheri.

Gwamna ya ce wanda suka mulki jihar a baya sun samu dama domin haka ya kamata su ba shi dama ya gudanar da mulkinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel