Ganduje: Kwamiti Ya Dauki Mataki Kan Zargin Badakala, Ya Fadi Tsare Tsaren Bincike

Ganduje: Kwamiti Ya Dauki Mataki Kan Zargin Badakala, Ya Fadi Tsare Tsaren Bincike

  • Yayin da ake ci gaba da binciken shugaban APC, Abdullahi Ganduje, kwamitin bincike ya magantu kan halin da ake ciki
  • Shugaban kwamitin, Mai Shari'a, Farouk Adamu ya ce suna sake yin duba kan kadarorin gwamnatin sa aka karkatar domin tabbatar da masu laifi
  • Wannan na zuwa ne bayan Gwamna Abba Kabir ya kafa kwamitin binciken badakalar kadarori a gwamnatin da ta gabata

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Kwamitin bincike da gwamnatin jihar Kano ta kafa ya bayyana matakin da zai dauka kan zargin badakalar Abdullahi Ganduje.

Kwamitin ya ce zai sake duba kan kadarorin da aka siyar da kuma karkatar da su ga wasu tsiraru na gwamnatin da ta gabata.

Kara karanta wannan

Ganduje vs Abba: Kwamiti ya bukaci Kanawa su kawo bayanan da za su taimaka

Kwamitin binciken Ganduje ya tabbatar da yin adalci yayin gudanar da aikinsa
Kwamitin binciken shugaban APC, Abdullahi Ganduje ya bayyyana tsare-tsaren da zai bi. Hoto: @officialAPCNg, @Kyusufabba.
Asali: Twitter

Ayyukan da kwamitin binciken Ganduje yake yi

Shugaba kwamitin, Mai Shari'a, Farouk Adamu shi ya bayyana haka a jiya Litinin 29 ga watan Afrilu a Kano, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Farouk ya ce daga cikin aikin kwamitin shi ne sake duba kan siyar da filayen idi da wuraren tarihi da gidaje da kuma makabartu a birnin mallakin gwamnatin jihar.

Ya ce za su yi bincike ko akwai almundahana yayin gudanar da su da kuma hukunta waɗanda ke da hannu a ciki.

Musabbabin kafa kwamitin binciken Ganduje

Har ila yau, Farouk ya ce ba a kafa kwamitin domin bita-da-kulli kan wani ba illa binciken gaskiya, cewar Leadership.

Alkalin ya ba da tabbaci ga al'umma cewa zai yi adalci yayin binciken Ganduje ba tare da nuna bambanci ba da sauran wadanda abin ya shafa.

Kara karanta wannan

An sanya ranar fara binciken Abdullahi Umar Ganduje a Kano

Ya bukaci al'umma da ke da wani shaida ko bayanai da za su taimakawa binciken da su rubuto domin tantancewa da gabatarwa.

'Yan siyasa da suka ɓata da ƴaƴansu

A wani labarin, mun kawo muku rahoton cewa akwai wasu 'yan siyasa da suka samu matsala da mahaifansu.

Mafi yawan 'yan siyasar na samun matsala da iyalansu kan bambancin jami'yya ko siyasa da ake samu a tsakani.

A wannan rahoton, Legit Hausa ta jero muku manyan 'yan siyasa a Najeriya da suka samu matsala da ƴaƴansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel