Sabon Rikici Ya Mamaye PDP, Shugabannin Jam’iyya Sun Dakatar da Dan Majalisar Tarayya

Sabon Rikici Ya Mamaye PDP, Shugabannin Jam’iyya Sun Dakatar da Dan Majalisar Tarayya

  • Shugabannin jam'iyyar PDP a gundumar Ngor, karamar hukumar Andoni ta jihar Ribas sun dakatar da Awaji-Inombek Abiante
  • Hon. Abiante shi ne dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Andoni/Opobo kuma mai biyayya ga Gwamna Siminilayi Fubara
  • A cewar shugabannin jam'iyyar ta zargi Abiante da shiga tsakani da wajen haifar da baraka a da sa hannu a kirkirar tsagin jam'iyyar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Ribas - Jam’iyyar PDP a Ngor, gunduma ta daya a karamar hukumar Andoni ta jihar Ribas ta dakatar da dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Andoni/Opobo, Awaji-Inombek Abiante.

Jam'iyyar PDP a jihar Ribas ta dakatar da dan majalisar tarayya
PDP reshen gundumar Ngor ta dakatar da dan majalisar tarayya, Awaji-Inombek Abiante. Hoto: @RepAbianteD
Asali: Twitter

PDP ta dakatar da dan majalisar tarayya

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da aka karantawa manema labarai bayan taron shugabanni da masu ruwa da tsaki na PDP da ya gudanar a ofishin jam’iyyar ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Cikakken sakamako: PDP ta lashe zaben dukan kujerun kananan hukumomi 33 a jihar Oyo

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abiante na daya daga cikin ‘yan majalisar tarayya mai biyayya ga gwamnan Ribas, Siminalayi Fubara, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kudurin ya samu sa hannun shugaban kwamitin riko na PDP a gundumar Ngor, Dike Bara da sakataren kwamitin, Dokubo Jackson, da wasu shuwagabanni 12.

Meyasa PDP ta dakatar da Abiate?

Da yake karantawa manema labarai kudurin, shugaban kwamitin, Bara ya ce an dakatar da Abiante ne saboda shiga tsakani da ya yi wajen haifar da baraka a jam’iyyar.

Ya kuma zargi dan majalisar da hannu wajen yada rigingimun jam’iyyar ba tare da izini ba da samar da wani tsagi na jam’iyyar a matakin gundumar da dai sauransu.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa jam’iyyar ta kuma zargi dan majalisar da karya sashe na 58, karamin sashe na 1 na kundin tsarin mulkin jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Shirin ba ɗalibai rancen kuɗi; Tinubu ya naɗa Jim Ovia a matsayin shugaban NELFund

An ruwaito cewa Abiate ya jagoranci zanga-zangar da wasu kungiyoyi suka yi na nuna adawa da yarjejeniyar da shugaban kasa ya cimma a rikicin siyasar jihar Ribas a watan Disamba.

Oyo: PDP ta lashe zaben kananan hukumomi

A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito cewa jam'iyyar PDP ta lashe dukkanin kujerun shugabannin kananan hukumomi 33 na jihar Oyo a zaben ciyamomin jihar da aka gudanar.

A yayin da PDP ke murnar samun wannan gagarumar nasarar, a hannu daya kuma jam'iyyar adawa ta APC a jihar ta ki amincewa da sakamakon zaben tana mai cewa an tafka kura-kurai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel