Dalibar da Ke Shirin Kammala Jami’a da Ta Bace Ta Rasu a Hatsarin Mota

Dalibar da Ke Shirin Kammala Jami’a da Ta Bace Ta Rasu a Hatsarin Mota

  • Dalibar jami'ar Abuja mai suna Murjanatu Zubairu da ta bata ranar Jumu'a da ta wuce ta rasu a hatsarin mota
  • Iyalan dalibar ne suka tabbatar da faruwar lamarin kuma sun ce ana shirye-shiryen mata janaza yau Talata
  • Hukumar kiyaye hadura ta kasa ta tabbatar da faruwar lamarin kuma ta bayyana yadda hatsarin ya faru

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja - Rahotanni da ke fitowa sun tabbatar da cewa dalibar jami'ar Abuja da aka sanar da bacewar ta satin da ya wuce ta rasu.

Murjanatu Zubair
Iyalan dalibar jami'ar Abuja sun sanar da rasuwarta a hatsarin mota. Hoto: Usman Garba Ibn Fodio
Asali: Facebook

Dalibar 'yar aji hudu mai suna Murjanatu Zubairu ta rasu ne a hatsarin mota bayan bacewarta ranar Jumu'a.

Kara karanta wannan

Shirin ba ɗalibai rancen kuɗi; Tinubu ya naɗa Jim Ovia a matsayin shugaban NELFund

Yadda aka sanu labarin rasuwar dalibar

Rahoton jaridar Daily Trust ya nuna cewa Alhaji Zubairu Jibrin Yewuti ne ya sanar da rasuwar dalibar a daren Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zubairu Jibrin Yewuti ya kara da cewa dalibar ta gamu ne da mummunan hatsarin mota a hanayar Lugbe zuwa Airport a Abuja.

Ya kuma tabbatar da cewa an gano gawarta ne a dakin ajiye gawa na asibitin koyarwa na jami'ar Abuja ne daga baya.

Karin rahotanni sun tabbatar da cewa ana sa ran binne dalibar a Abuja ne a yau Talata, 30 ga watan Afrilu.

Bayanin hukumar FRSC kan hadarin

Hukumar kiyaye hadura ta kasa ta tabbatar da faruwar hatsarin ta bakin kwamandan ta, Sunday Ajokotola, cewar jaridar Punch

Ya tabbatar da cewa mutane 10 ne hatsarin ya ritsa da su inda hutu suka mutu ta hanyar konewa, ciki har da dalibar.

Kara karanta wannan

EFCC ta gurfanar da Yahaya Bello bisa zargin karkatar da Naira biliyan 80

Ya kuma kara da cewa hatsarin ya faru ne da dare kusa da cocin Dunamis da ke kan hanyar Lugbe a Abuja.

A cewar kwamanda Sunday, kafin isan ma'aikatan bada agaji, mutum shida sun samu kuna sosai kuma su suka kai waɗanda suka rasu asibitin Abuja.

Hatsari ya lakume rai 19 a Kogi

A wani rahoton, kun ji cewa wani mummunan hatsarin mota da ya auku a jihar Kogi ya yi sanadiyyar salwantar da rayukan mutum 19 har lahira.

Hatsarin motan ya auku ne bayan wata motar Dangote ta yi taho-mu-gama da wata motar bas mai ɗauke da fasinjohi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel