Latest
'Yan jarida na taka rawa wajen samar da bayanai da rahotanni ga al'umma. Sai dai akwai kasashen da ba su da cikakken 'yancin gudanar da ayyukansu cikin walwala.
Dubunnan mambobin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Jigawa sun watsar da jam'iyyar inda suka sauya sheka zuwa jam'iyyar adawa ta NNPP.
Shugaban jam'iyyar APC, Dakta Abdullahi Umar Ganduje yace sauyin yanayi da rashin ilimi a tsakanin al'ummar Fulani shi ne babban abin da ya jefa Arewa a matsala.
Yayin da matsalar safarar kwayoyi ta addabi kasar Najeriya, Majalisar Dattawa ta amince da dokar hukuncin kisa kan masu mu'amala da siyar da kwayoyi .
Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi ya nada tsohon gwamnan jihar, Sa'idu Dakingari a matsayin Amirul Hajji na wannan shekara domin jigilar mahajjata.
Fadar shugaban kasa ta saki bidiyon Bola Ahmed Tinubu yana tafiya zuwa ofis dinsa tun bayan dawowarsa gida Najeriya daga ziyarar da ya kai kasashen waje.
Gwamnan jihar Rivers Siminalayi Fubara ya ziyarci majalisar dokokin jihar Rivers yayin da ake batun 'yan majalisar sun fara yunkurin tsige shi daga kan kujerarsa.
Hatsarin iskar gas ya yi sanadiyyar mutuwar mutane biyu a Lagos tare da jikkata mutane uku. Rundunar yan sanda jihar sun tabbatar da faruwar lamarin.
An shiga jimami a unguwar Gama B dake jihar Kano bayan an tsinci gawar wani magidanci, Bello Bukar Adamu a karamar hukumar Kumbotso da ya bar gida ranar Lahadi.
Masu zafi
Samu kari